Kasuwanci
Afirka ta Kudu za ta fito da tsarin biyan tara don haɓaka ayyukan yi ga baƙaƙen fata
Dokar samar wa baƙaƙen fata ayyukan yi ta shekarar 2003 ta ƙarfafa gwaiwar kamfanoni su ringa ɗaukar baƙaƙen fata aiki tare da ƙara musu girma ta hanyar sassauta musu haraji da kuma damar samun ƙwangilolin gwamnati.Karin Haske
Nijeriya na cikin halin tsaka-mai- wuya kan ƙara haraji ga masu hannu da shuni
Ƙudurin Nijeriya na ƙara harajin da matsakaita da masu hannu da shuni za su biya don samun ƙarin kudaɗen shiga da nufin samar da ci gaba a ƙasar ya janyo ce-ce-ku-ce game da yiwuwar matakan aiwatar da shi da kuma yin adalci.Kasuwanci
Matatar Dangote ta ƙaryata zargin rashin ingancin sinadarin da take amfani da shi don samar da fetur
Kamfanin Dangote ya tabbatar da cewa sanadarIn da matatar mansa yake amfani suna da inganci, hakan ya biyo binciken da kwamitin majalisar wakilai ya soma kan zargin rashin ingancin kayayyakin da kamfanin yake amfani da su wajen samar mai a Nijeriya.Afirka
Jami'an gwamnatoci a Nijeriya sun karɓi Naira biliyan 721 a matsayin cin hanci a 2023 — NBS
A jimulla an ƙiyasta cewa an biya kusan Naira 721 biliyan (dalar Amurka biliyan 1.26) a matsayin cin hanci ga jami’an gwamnatocin a Nijeriya a shekarar 2023, adadin da ya kai kashi 0.35 cikin 100 na ƙudaɗen (GDP) na ƙasar, in ji sabon rahoton NBSKasuwanci
NNPC ya ƙaryata rahoton zargin ya yi ƙarin N3.3tr a kuɗin tallafin man fetur
Kamfanin NNPC ya ce yana gudanar da harkokin kasuwancinsa ne bisa gaskiya da amana ta hanyar bin ƙa'idojin ƙasashen duniya kana babu wani lokaci da kamfanin ya taɓa ƙara kuɗin tallafin man fetur na gwamnatin tarrayar Nijeriya.
Shahararru
Mashahuran makaloli