Shugaban majalisar mulkin sojin Sudan Abdel Fattah al Burhan ya ce '''Yan mulkin-mallaka'' ne suke kara rura wutar rikici a Afirka.
Al Burhan ya bayyana haka ne a yayin ganawarsa da shugaban ƙasar Guinea Bissau Umaro Sissoco Embalo a fadar shugaban ƙasa da ke Bissau babban birnin ƙasar, a cewar wata sanarwa da majalisar ta fitar a ranar Lahadi.
Majalisar ta ce Al Burhan da Embalo sun gudanar da wani taron ƙoli na ƙasashen biyu da zummar tattauna kan batutuwan da suka shafi ƙasashen biyu da kuma hanyoyin inganta haɗin-gwiwa a dukkan fannoni da suka shafe su.
Al Burhan ya kuma taɓo halin da ake ciki a Sudan, musamman kan tawayen da dakarun kai ɗaukin gaggawa na RSF suke yi kan gwamnati da sauran cibiyoyinta, a cewar sanarwar.
"Akwai 'ƙasashen 'yan mulkin-mallaka da ke aikin rura wutar rikici a nahiyar Afirka," in ji shi.
Ya ƙara da cewa "A halin da ake ciki yanzu, Afirka ta farka, kuma hakan ya ba da damar yin adawa da tsoma bakin ƙasashen waje a harkokin da suka shafi nahiyar. Muna yaba ƙokarin wasu ƙasashen Afirka, waɗanda suka yi tsayin daka wajen adawa da mulkin-mallaka zamanin baya da na yanzu.''
Embalo ya bayyana fatan samun zaman lafiya a Sudan cikin gaggawa, a cewar sanarwar.
A ranar Lahadi ne dai shugaba Al Burhan ya isa ƙasar Guinea-Bissau, ƙasa ta biyu a rangadin da yake yi a Afirka, wanda ya fara daga Mali a ranar Asabar kana ana sa rai zai je Saliyo da Senegal a nan gaba.