Yarjejeniyar wadda aka saka wa hannu da kamfanin dillancin labaran AFP ya samu gani ta yi kira ga a samar da gwamnatin dimokuraɗiyya mai ‘yanci da adalci ba tare da nuna bambancin addini ko ƙabila ko yanki ba. / Hoto: AA

Rundunar RSF ta Sudan tare da haɗin gwiwar wasu ƙungiyoyi na siyasa da masu ɗauke da makamai sun ƙulla wata yarjejeniya domin kafa gwamnatin adawa a ƙasar da ke fama da rikici, kamar yadda wasu majiyoyi suka tabbatar a ranar Lahadi.

“An kammala,” kamar yadda majiya da ke kusa da waɗanda suka sa hannu kan yarjejeniyar wadda aka yi a Nairobi ta bayyana wa kamfanin dillancin labarai na AFP.

Matakin dai ya zo ne bayan shafe kusan shekaru biyu RSF ɗin na gwabza kazamin yaki da sojojin ƙasar, lamarin da ya yi sanadiyyar korar mutane fiye da miliyan 12 tare da haifar da abin da Majalisar Dinkin Duniya ta bayyana rikicin da ya fi haddasa yunwa da raba mutane da muhallansu a tarihi.

Daga cikin waɗanda suka saka hannun akwai ɓangaren Jam’iyyar Sudan Peopl’es Liberation Movement-North (SPLM-N) ƙarƙashin jagorancin al-Hilu da ke da iko da kudancin Jihar Kordofan da Blue Nile.

Abdel Rahim Dagali wanda ƙane ne kuma mataimakin kwamandan RSF Mohamed Hamdan Dagalo – shi ma ya saka hannu duk da bai halarci wurin ba.

Yarjejeniyar wadda aka saka wa hannu da kamfanin dillancin labaran AFP ya samu gani ta yi kira ga a samar da gwamnatin dimokuraɗiyya mai ‘yanci da adalci ba tare da nuna bambancin addini ko ƙabila ko yanki ba.

AFP