Kyaftin Ibrahim Traore ya kwace mulki a Burkina Faso a farkın shekarar 2022. Hoto: AA.

Shugaban mulkin sojin Burkina Faso Kyaftin Ibrahim Traore ya kori Firaministan ƙasar Apollinaire Joachim Kyelem de Tambela da kuma rusa gwamnatin ƙasar kamar yadda aka karanto a wata sanarwa a talabijin ɗin ƙasar a ranar Juma’a da dare.

Sanarwar ta bayyana cewa “mambobin gwamnatin da aka sauke za su ci gaba da gudanar da ayyukansu har sai an kafa sabuwar gwamnati.”

Matias Traoré, wanda shi ne babban sakataren gwamnati da kuma majalisar ministoci shi ne ya karantar sanarwar a talabijin.

A Mali ma an samu irin haka inda a ranar 11 ga watan Nuwamba Janar Assimi Goita ya sallami Firaminista Choguel Kokalla Maiga kwanaki bayan firaministan ya caccaki gwamnatin ƙasar.

Burkina Faso da Mali da Nijar sun kafa ƙungiyar haɗaka mai suna Sahel Alliance a Satumnbar 2023 tare da sanar da kafa ƙungiya ta musamman ta soji wadda za ta yaƙi ‘yan ta’addan da suka addabi yankin.

TRT Afrika