Ƙarin farashin kuɗin kayan masarufi ya haifar da sabbin alƙaluman hauhawar farashin kayayyaki a Nijeriya. / Hoto: Reuters  

Alƙaluman hauhawar farashin kayayyaki a Nijeriya ya karu zuwa kashi 33.88 a watan Oktoban 2024, adadin da ya nuna an samu ƙarin kashi 1.18 cikin dari daga kashi 32 cikin 100 da aka samu a watan Satumban 2024.

Bayanan da Hukumar Ƙididdiga ta Nijeriya (NBS) ta fitar a ranar Juma’a sun nuna cewa an samu ƙaruwar hauhawar farashin sufuri da kuma kayayyakin masarufi a ƙasar.

“Alƙaluman hauhawar farashin kayan masarufi a watan Oktoban 2024 ya kai kaso 39.16 cikin 100, ƙarin kaso 7.64 cikin 100 kan adadin da aka samu a watan Oktoban 2023 (31.52%),” in ji NBS.

Hukumar ta ƙara da cewa an samu ƙari a farashin kayayyakin abinci kamar masara da shinkafa da hatsi da kuma man girƙi, waɗanda suka kara yawan hauhawar farashin abinci da ake samu a kowane shekara.

Rikicin tattalin arziki

Kazalika alƙaluman sun nuna yanda hauhawar farashin kayayyaki yake ta ƙaruwa a shekarar 2024.

A watan Yuni an alƙaluman hauhawar farashin ya aru zuwa kaso 34.19 cikin 100, adadin da ya zarce na watan Mayun na kashi 33.95 cikin 100.

'Yan Nijeriya suna fuskantar ɗaya daga cikin mafi munin tabarbarewar tattalin arziki da aka taba gani a tsawon shekaru da dama, inda tsare-tsaren kuɗi a ƙasar suka sanya darajar Naira take ci gaba da faɗuwa idan aka kwatanta da dala.

Jim kaɗan bayan hawansa kan mulki a watan Mayun bara, Shugaba Bola Tinubu ya bayyana kawo ƙarshen tallafin man fetur, wanda ya ce gwamnati ba za ta iya zure ci gaba da biya ba.

Lamarin dai ya fusata al'ummar Nijeriya kana ya haifar da zanga-zanga a faɗin ƙasar.

Ko da yake dai, masu sharhi sun bayyana cewa ba a tanaɗin isassun matakan da za su taimaka wajen rage raɗaɗin sakamakon sauye-sauyen da aka yi ba.

TRT Afrika