Farashin Bitcoin ya haura sama da $80,000 a karon farko a 2024 / Hoto: Reuters

Farashin cinikin kuɗin kirifto na Bitcoin, ya yi tashin da ba a taɓa gani ba inda ya kai har dala 82,022.98, a cewar kamfanin hada-hadar kudaɗen kirifto na Coindesk.

Fitaccen kuɗin intanet ɗin ya yi wannan tashin ne bayan sake zaɓen tsohon shugaban Amurka Donald Trump, wanda ya yi na'am da kuɗaɗen kirifto kana ya yi alƙawarin mayar da Amurka babban birnin kirifto na duniya.

"Akwai yiwuwar Bitcoin da sauran kudaɗen kirifto su rikiɗe zuwa manyan kadarori a nan gaba,'' kamar yadda mai fashin baƙi na kamfanin saka hannun jari na ByteTree Charles Morris ya shaida wa kamfanin dillacin labarai na Faransa, AFP.

A ranar Larabar da ta wuce ne, farashin kuɗin Bitcoin ya kai dala 75,000, adadin da ya ƙaru daga dala 73,797.98 da aka samu baya a cikin watan Maris.

"Muna sa ran farashin zai ci gaba da hawa har zuwa wani lokaci- kamar zuwa shekara ɗaya. Fatanmu shi ne ya kai dala 100,000,'' Stephane Ifrah daga kamfanin hada-hadar kudaɗen kirifto na Faransa Coinhouse ya shaida wa AFP.

Ana kallon Trump a matsayin ɗan takarar da ke goyon bayan kudin kirifto a fafatawarsa da abokiyar hamayyarsa Kamala Harris a zaɓen Amurka da aka gudanar a makon jiya.

A baya dai, lokacin mulkinsa na farko, Trump ya bayyana kudaden kirifto a matsayin zamba, sai dai tuni ya sauka daga wannan matsayin, har ma ya ƙaddamar da nasa shafin dandalin kuɗaɗen.

AFP