Gwamnatin mulkin sojin Jamhuriyar Nijar, ƙarƙashin jagoranci Janar Abdourrahmane Tiani ta sanya hannu kan wata doka ta wucin-gadi wadda ta soke shaidar zama ɗan ƙasa a wasu ‘yan Nijar biyu.
A ranar Litinin 6 ga watan Janairun 2025 ne Shugaba Tiani ya sanya hannu kan dokar, kamar yadda jaridun ƙasar ciki har da Actu Nijar suka rawaito.
Ana zargin mutanen biyun da suka haɗa da Maman Sani Ali Adam, wanda aka fi sani da Celon Ali Adam, da Boussada Ben Ali da aikata ayyukan da ke barazana ga zaman lafiyar jama'a, ciki har da yaɗa bayanai da ke tayar da ƙura da kuma kalaman wariyar launin fata, da na ɓangaranci, da kuma ƙyamar baki.
Kazalika ana zarginsu da kasancewa na hannun daman hamɓararren shugaban ƙasar Mohamed Bazoum.
Matakin ya biyo bayan dokar rajistar da aka rattabawa hannu a watan Agustan 2024, wadda ta ba da damar shigar da sunan duk wani mutum da ake zargi da hannu cikin ayyukan ta'addanci da barazana ga zaman lafiya da kuma cin amanar ƙasa.
Kazalika dokar ta tanadi tattara sunayen waɗanda ake zargi, tare da ƙwace kadarorin mutum, tare da hana shi tafiye-tafiye da kuma kwace shaidar zama ɗan ƙasa ta Nijar.
Sabon matakin dai ya biyo bayan jerin ire-iren ayyukan da gwamnatin mulkin soji Nijar (CNSP) take ɗauka na samar da sauyi a ƙasar.
A watan Oktoban 2024 ne aka ƙwace shaidar zama ɗan ƙasa ta tsohon ƙaramin minista a fadar shugaban ƙasar Rhissa Ag Boula da kuma wasu mutum takwas na hannun daman hamɓararren shugaban ƙasar Mohamed Bazoum.
An zarge su ne da laifin cin amanar ƙasa, da yaɗa bayanan sirri ga wasu ƙasashen waje da kuma shiga ayyukan ta'addanci.