Gwamnatin ƙasar Senegal ta samu rancen dala miliyan 300 daga kasuwannin duniya, da nufin biyan buƙatun kuɗinta na cikin gida bayan da Asusun ba da Lamuni na IMF ya ɗage lokacin da ya kamata ya ba wa ƙasar rancen, a cewar wata sanarwa gwamnati a ranar Laraba.
A Satumba ne aka gabatar da sakamakon binciken da aka gudanar kan kuɗaɗen gwamnati a ƙasar da ke yammacin Afirka, watanni shida kenan bayan hawan shugaba Bassirou Diomaye Faye kan mulki, inda firaminista Ousmane Sonko ya bayyana lamarin a matsayin ''wani bala'i.''
An samu gibi a kasafin kuɗin da gwamnati ta gudanar da bincike kanss, da kaso 10.4 cikin 100 na GDP na ƙasar, maimakon kashi 5.5 cikin 100 da gwamnatin da ta gabata ta sanar.
Bashin da ake bin ƙasar ya kai kashi 76.3 cikin 100 na GDP, kamar yadda binciken ya nuna, maimakon kaso 65.9 cikin 100 da aka sanar a baya.
'Sauya alƙaluman kuɗaɗe'
Firaminista Sonko ya zargi tsohuwar gwamnatin Senegal da sauya alƙaluman kuɗaɗen da aka bai wa abokan hulɗar ƙasa-da-ƙasa, ciki har da IMF, lamarin da shugabannin baya suka musanta.
Asusun na IMF ya ce a tsakiyar watan Oktoba ne ya fara tantance tasirin binciken da aka yi, a shirye-shiryen da suka gabata da kuma waɗanda ake shirin aiwatarwa ƙarƙashin yarjejeniyar da aka cim ma a shekarar 2023.
Kafofin yaɗa labarai sun ruwaito ministan kuɗi na Senagal, Cheikh Diba yana cewa IMF ya dakatar da shirin ba da tallafi na dalar Amurka biliyan 1.8, kana an ɗage lokacin bayar da kusan dala miliyan 559 wa ƙasar zuwa shekarar 2025.
Sai dai IMF bai ba da tabbacin hakan ga AFP ba, a lokacin da yake amsa tambayoyi,
Tara dala miliyan 300
A wata sanarwa da ma'aikatar kuɗi ta ƙasar ta fitar a ranar Laraba ta ce, ƙasar Senegal ta tara dala miliyan 300 daga kasuwannin duniya "domin ta samu damar biyan buƙatunta na cikin gida, saboda ɗage lokacin da aka tsara IMF zai bai wa ƙasar kuɗaɗen tun farko."
Bankin Amurka JP Morgan ne ya sa hannu kan yarjejeniyar bashin da aka ƙarba wanda za a ba da kuɗin ruwa na kashi 6.33 cikin100, in ji sanarwar.
Tuni dai Senegal ta samu bashin dala miliyan 750 daga Eurobonds a watan Yuni, kana za ta biya kuɗin ruwa na kaso 7.75 cikin 100.
"Nasarar tara waɗannan kuɗaɗe ya nuna irin ƙwarin gwiwar da aka sake samu daga masu saka-hannun jari daga ƙasashen duniya a Senegal", in ji sanarwar ma'aikatar, tana mai ƙari da cewa hakan zai kasance rance na ƙarshe da Senegal za ta ƙarba daga kasuwannin duniya a shekarar 2024.
Rage darajar rance
Gwamnati "na shirin tattaunawa da IMF don samar da wani sabon shiri" da nufin daidaitawa da kuma samar da cigaba, in ji sanarwar.
Cibiyar Moody's ta rage darajar matsayin rancen Senegal bayan kammala binciken kuɗaɗen bashin da ƙasar ta karɓa, tare da sanya ta ƙarƙashin waɗanda ake saka wa ido.