Daga Brian Okoth
Shugaban Botswana Duma Boko ya naɗa Bogolo Kenewendo a matsayin Ministar Ma'adinai ta ƙasar, wani muhimmin muƙami da ya ɗora mata alhakin kula da masana'antar daimon da Botswana ta ke ji da ita.
A 'yan kwanakin baya ne aka rantsar da Kenewendo a matsayin zababbiyar 'yar majalisar dokokin Botswana ta musamman.
Ta samu wannan matsayi ne a inuwar jam'iyyar Umbrella for Democratic Change (UDC), wadda shugaba Boko ya tsaya takara ƙarkashinta a zaɓen Botswana na ranar 30 ga watan Oktoba.
A baya dai, Kenewendo mai shekaru 37 ta taba riƙe mukamin minista a gwamnatin tsohon shugaban ƙasar Mokgweetsi Masisi.
Tsohuwar 'yar Majalisa
Tana da shekaru 30 a duniya lokacin da Shugaba Masisi ya naɗa ta matsayin ministar harkokin zuba jari da kasuwanci da kuma masana'antu a watan Afrilun 2018.
Kenewendo ta riƙe muƙamin har zuwa watan Nuwamba na 2019.
Kafin lokacin, ta taba zama zababbiyar ‘yar majalisa ta musamman daga shekarar 2017.
Tsohuwar jam'iyyar da ta riƙe mulki a ƙasar, Botswana Democratic Party (BDP) - ƙarkashin shugaban ƙasa na lokacin Ian Khama - ita ce jam'iyyar da ta fara baiwa Kenewendo damar samun matsayi a majalisar dokokin ƙasar shekaru bakwai da suka wuce.
Muhimmiyar ma'aikata
A lokacin da take riƙe da mukamin ministar harkokin kasuwanci, ta mai da hankali ne wajen inganta hanyoyin sauye-sauyen tattalin arziki, da jawo masu saka hannayen jari daga ƙasashen waje da kuma kara haɓaka tattalin arzikin Botswana.
Tuni dai shugaba Boko ya miƙa mata amanar kula da ma'aikatar ma'adinai mai matukar muhimmanci a ƙasar.
Ma'aikatar ma'adinai ta Botswana tana samar da kusan kashi 40 cikin 100 na kuɗaɗen shigar gwamnatin ƙasar, inda dutsen daimon ya kasance muhimmin albarkatun ƙasar.
Botswana wacce ke samar da kashi 20 cikin 100 dutsen daimon a duniya, ita ce ƙasar da ta fi kowace kasa samar da dutsen daimon a Afirka.
Kaso 80 cikin 100 na kayayyakin da ake fitar wa zuwa ƙasashen
A duniya baki ɗaya, Botswana na matsayi na biyu, bayan Rasha.
A cewar IMF, Botswana na fitar da kusan kashi 80 cikin 100 na daimon ɗinta zuwa ƙasashen duniya, kana kashi uku na tattalin arzikin ƙasar.
A shekarar 2022, kasar da ke yankin Afirka ta Kudu ta fitar da dutsen daimon ɗinta da darajarsu ta kai dala biliyan 7.4.
Waɗannan alƙaluma suna nuna muhimmacin ma'aikatar da Kenevendo za ta jagoranta.
Ci gaba mai ban sha'awa
Ta yi digiri na biyu a fannin tattalin arziki na ƙasa da ƙasa a Jami'ar Sussex da ke ƙasar Ingila, sannan tana da digiri a fannin tattalin arziki a jami'ar Bostwana.
Bayan kammala karatun digirin digirgir ɗinta na biyu a shekarar 2016, an ɗauke ta aiki a matsayin mai ba da shawara a Botswana, daga nan kuma ma'aikatar ciniki da masana'antu ta Ghana ta ɗauke ta a matsayin gwararriya a fannin tattalin arziki.
Ta yi aiki a Ghana na ɗan ƙanƙanin lokaci, sannan ta koma Botswana, inda aka zaɓe ta a matsayin 'yar majalisa a shekarar 2017. A lokacin zamanta a majalisar, ta ɗauki nauyin ƙudurin dokar kula da yara da mata.
'Shugabancin matasa a Afirka ba sabon abu bane'
Yanzu kuma nauyin aikin ministar ma'aikatar ma'adinai ta ƙasar ya rayata a wuyanta.
Fitattun kalaman Kenewendo, kamar yadda shaida wa Majalisar Dinkin Duniya, su ne: "Idan kuka kalli tarihi da kyau, za ku gane cewa shugabancin matasa a Afirka ba sabon abu ba ne."
A ranar Alhamis, 14 ga watan Nuwamba, shugaba Bako ya kuma naɗa wasu ƙarin ministoci biyar.
Waɗanda aka nada sun haɗa da Nelson Ramaotwana, wanda zai kula da ma’aikatar shari’a, sai Ketlhalefile Motshegwa wanda zai kula da harkokin ƙananan hukumomi, da Tiroyaone Ntsima na ma’aikatar kasuwanci, da David Tshere na ma'aikatar sadarwa da kuma Manjo-Janar Pius Mokgware mai ritaya na ma'aikatar ƙwadago .
Mataimakin shugaban ƙasa ne yake rike da matsayin ministan kuɗi
A farkon makon nan ne, shugaba Bako ta naɗa ministoci shida a gwamnatinsa, waɗanda suka haɗa da sarauniyar ƙyau ta Botswana a shekarar 2022 Miss Lesego Chombo, wadda aka bata muƙamin ministar matasa da harkokin jinsi na ƙasar.
Sauran ma'aikatun da aka naɗa musu sabbin ministoci sun hada na lafiya, da noma, da na walwalar yara, da kuma na harkokin ƙasashen waje.
Mataimakin shugaban ƙasa Ndaba Gaolathe ne yake riƙe da matsayin ministan kuɗi na Botswana.