An buɗe matatar man Dangote a 2023 a Legas inda ake sa ran cewa za ta taimaka wa matatun man ƙasar. / Hoto: Reuters

A watan Janairun 2024 ne matatar man da biliyoniya dan Nijeriya Aliko Dangote ya samar a Legas da ke da karfin sarrafa ganga 650,000 kowace rana, ta fara tace danyen mai zuwa man diesel, naptha da ma jirgin sama, inda a watan Satumba ta fara samar da man fetur.

Tana da manufar gogayya da matatun mai na Turai idan ta fara cikakken aiki, amma tana ta fama da karancin samun danyen mai a cikin gida Nijeriya.

Edwin Devakumar, shugaban matatar mai ta Dangote ya ce a yanzu matatar na aiki da kashi 85 ne inda nan da kwanaki 30 za ta fara cikakken aiki dari bisa dari.

A shekarar da ta gabata, matatar ta fara sayo danyen mai daga kasashen waje saboda gaza samun isasshe duk da yarjejeniyar da suka kulla da gwamnatin Nijeriya na sayen danyen man da Naira.

Matatar mai ta Dangote na neman sabbin kasuwannin sayar da albarkatun manta. Wand aya samar da matatar Aliko Dangote ya fada wa wani taron ƙwararru na Nijeriya da suka ziyarci matatar makon d aya gabata cewa suna aika wa da man jirgin sama a jiragen ruwa biyu zuwa ga kamfanin mai n Aramco da ke Saudiyya.

"Muna neman shiga dukkan kasuwanni a yanzu haka," in ji Devakumar.

Reuters