Gwamnatin kasar Ghana ta bayyana cewa ta samu karuwa a adadin zinaren da take da shi a bana.
Gwamnan Babban Bankin Ghana, Dakta Ernest Addison ne ya sanar da hakan a lokacin taro karo na hudu kan batun haka da fitar da zinarin Ghana.
Kamfanin dillancin labarai na Ghana ya ruwaito gwamnan babban bankin yana cewa an samu karuwa da sama da tan 7.70 na zinaren.
Ya bayyana cewa an samu kashi 80 na zinaren daga manyan kamfanonin hakar ma’adinai sai kuma sauran kashi 20 din daga kananan masu hako ma’adinai na kasar.
Ya ce an samu karin ta hanyar shirin sayar da zinare na cikin gida wanda aka fito da shi a 2021 domin kara adadin zinarin da ke babban bankin kasar ta hanyar sayen zinaren da aka haka a cikin gida da kudin kasar.
Ya bayyana cewa kafin fito da wannan shirin a 2021, adadin zinaren da Ghana ke da shi a tsawon shekaru bai wuce tan 8.77 ba, inda ya ce burin bankin shi ne ya rubanya adadin zuwa 17.4 a cikin shekara biyar.
Dakta Ernest ya bayyana cewa wannan karuwar da Ghana ta samu zai matukar taimaka mata wurin habakar tattalin arzikinta.
Ghana ce kasar da ta fi kowace kasa arzikin zinare a Afirka. Ko a kwanakin baya sai da gwamnatin kasar ta fitar da sanarwa inda ta ce adadin zinaren da aka fitar a 2022 ya kai yawan nauyin ounce miliyan 3.08, sama da nauyin ounce miliyan 2.72 da aka fitar a shekarar 2021.