Tsohon Shugaban Nijeriya Olusegun Obasanjo kana shugaban hukumar yammacin Afirka kan kwayoyi, Olusegun Obasanjo /Hoto:Reuters

Tsohon Shugaban Nijeriya Olusegun Obasanjo ya bukaci kasashen Afirka da su ci moriyar yarjejeniyar kasuwanci mara shinge ta Afirka wato African Continental Free Trade Area (AfCFTA) don kawo karshen mulkin-mallakar da ke kawo cikas ga bunkasar tattalin arzikinsu.

Tsohon shugaban ya bayyana hakan ne lokacin wani taro da aka yi kan matasa da shugabanci wato African Youth and Governance Convergence (AYGC) wanda aka yi a garin Mankessim da ke kasar Ghana, kamar yadda kamfanin dillancin labarai na Ghana ya rawaito.

Ya ce dole sai kasashen Afirka sun kauce wa sabon nau'in mulkin-mallaka da sunan "wasu tsare-tsaren masu kyau" daga Asusun Bayar da Lamuni na Duniya (IMF) da Bankin Duniya da kuma Majalisar Dinkin Duniya.

Har ila yau ya ce yarjejeniyoyin da aka sanya wa hannu da suka fito daga cibiyoyin kasashe masu mulkin-mallaka kan ciniki da kasuwanci ba a tsara su saboda ci-gaban Afirka ba.

Labari da za ku so ku karanta: ‘Yan Nijeriya makiya a gida, masoya a waje – Obasanjo

"Idan kasashen Afirka suka ci gaba da dogaro kan manyan cibiyoyin kudin duniya a matsayin hanyar kai wa ga ci gaba, nahiyar ba ta samu nasara ba duk da dimbin arzikin da take da shi," in ji tsohon Shugaba Obasanjo.

Ya ci gaba da cewa sakamakon dogaro da su shi ne ya kawo "tsananin talauci da bakar yunwa da kuma rashin aikin yi," a cewarsa.

An fara taron ne a ranar Asabar 12 ga watan Agusta kuma za a kwashe tsawon mako daya ana yinsa, inda wakilai 65 daga kasashen Afirka 27 da Amurka da kuma Kanada suke halarta.

An kulla yarjejeniyar kasuwanci mara shinge tsakanin kasashen Afirka wato (AfCFTA) a birnin Kigali na kasar Rwanda a shekarar 2018, kuma ta fara aiki ne a watan Mayun shekarar 2019.

TRT Afrika