Kamfanin jirgin saman Turkish Airlines ya bayyana gagarumin ci-gaban kasuwancin da ya samu a watan Mayu inda ya yi jigilar mutum miliyan 7.4, a cewar alkaluman da ya aike wa Hukumar Bayyana Harkokin Kasuwanci ta Turkiyya (KAP).
Hakan ya nuna cewa an samu karuwa da kashi 16 cikin dari idan aka kwatanta da fasinja miliyan 6.4 da kamfanin ya dauka a watan Mayu na 2022.
Kamfanin jiragen saman ya samu karuwar kashi 11.3 na fasinjojin kasashen duniya a shekara, inda ya dauki fasinja miliyan 4.5 a watan Mayu. Adadin fasinjojin da ya dauka a cikin kasar ya karu zuwa kashi 24.4 wato fasinja miliyan 2.9 a watan da ake magana a kansa.
Kazalika adadin kujerun da aka yi amfani da su a cikin jirgin ya karu zuwa kashi 81.8 a watan na Mayu -- kashi 80.7 a jiragen da suka yi jigila a cikin kasa da kuma kashi 82 na wadanda suka yi jigila zuwa kasashen waje. A watan Mayun 2022, adadin shi ne kashi 80.
Ya zuwa karshen watan Mayu, kamfanin yana da jiragen 417, a cewar alkaluman.
Alkaluman wata biyar
Daga Janairu zuwa Mayu, kamfanin jiragen saman ya dauki fasinja miliyan 31, kari da kashi 29 idan aka kwatanta da bara.
Jigila zuwa kasashen waje ta karu da kashi 49.2 a shekara wato kamfanin ya dauki mutum miliyan 11.6 a wata biyar.
Haka kuma kujerun da fasinja suka zauna sun karu da kashi 81.1 a watanni biyar na farkon wannan shekarar, a cewar sanarwar.
Sai dai adadin kayan da jiragen ke dauka ya ragu da kashi 9.6 zuwa kusan tan 608,100 daga Janairu zuwa Mayu.