Manoma sama da 5,000 ne suka ci moriyar wannan tallafi a yankin Gomao Ta tsakiya a Ghana. Hoto / Ghana News Agency

Sama da manoma 5,000 daga gundumar Gomoa ta tsakiya a kasar Ghana ne suka ci moriyar shirin tallafin kayayyakin noma daga gwamnatin kasar da nufin inganta ayyukansu da kuma habaka hanyoyin samun riba a kasuwanni.

Kayayyakin da aka ba manoman sun hada da adduna 6,000 da buhun taki 1,000, da kwalaye maganin kashe kwari da ciyayi guda 800 da kuma takalman ruwa masu rufi guda 2,500, kamar yadda kamfanin dillancin labarai na kasar GNA ya rawaito.

Yayin bikin mika kayayyakin a karshen makon jiya, shugaban gundumar yankin Gomao ta tsakiya Mista Benjamin Kojo Otoo ya ce asusun bai-daya na Majalisar dokokin kasar ne ya sayo kayayyakin don taimaka wa manoma don su samu damar inganta amfanin gonakinsu.

Ma'aikatar aikin noma ta gundumar Gomao ce ta zabo manoman da suka ci moriyar wannan shiri domin tabbatar da an rarraba kayayyakin cikin adalci da kuma kauce wa korafe-korafe da rashin gamsuwa daga al'umma, a cewar GNA

Kazalika, shirin gwamnatin Ghana na shuka itatuwa 200,000, ya bai wa manoman 'ya'yan itatuwa da suka hada da kwakwar manja da kwakwa da mangwaro da sauransu don kasar ta iya fitarwa zuwa kasashen ketare da kuma karkara.

''Gwamnati za ta ci gaba da samar da yanayi mai kyau don samar da amfanin gona mai kyau tare da samar wa manoma takin zamani da sinadarai da za su inganta tsiro da 'ya'yan suka na kayan lambu don kara bunkasa ayyukan noma a gundumar,'' a cewar Mista Otoo.

Ya kara da cewa gwamnatin shugaban Akufo-Addo ba za ta taba yin kasa a gwiwa ba wajen ganin ta inganta harkar noma, ya kuma bukaci manoma da su yi hattara da alkawuran wasu ‘yan siyasa da ba sa iya cikawa.

Ya kuma jaddada batun karin farashin samar da koko da gwamnati ta yi a baya-bayan nan, ''hakan na daya daga cikin mafi kyawun mataki da gwamnati ta dauka don inganta rayuwar al'ummarta.

Mataimakiyar ministan harkokin cikin gida a Ghana kuma yar' majalisa mai wakiltar yankin Gomoa ta tsakiya Madam Naana Eyiah Quansah, ta bai wa manoman tabbacin cewa gwamnati ta shirya tsaf domin zuba jari a fannin noma, kuma za ta ci gaba da samar da kayayyakin amfanin gona kyauta domin ciyar da ayyukansu da rage wahalhalun tattalin arziki da ake fuskanta a kasar, kamar yadda GNA ya bayyana.

TRT Afrika