Gwamnatin tarayyar Nijeriya ta kaddamar da shirin aiwatar da bunkasa ayyukan noma na Agro Pocket a jihohi biyar da ke fadin kasar.
An dai kaddamar da shirin ne a karamar hukumar Bunkure da ke jihar Kano a ranar Litinin.
Manoma 60,000 ne za su ci moriyar tallafin kayayyakin aiki kamar taki da magungunan kashe ciyayi da kwari, a jihohi biyar din da suka hada da Kano da Neja da Kebbi da Jigawa, da kuma Sokoto.
Shirin wanda ya mayar da hankali wajen inganta ayyukan kananan manoma a Nijeriya ta hanyar samar musu da kayayyakin aiki na zamani, don kara yawa da abinci da samar da abinci mai gina jiki da ake samarwa a kasar.
Aikin yana karkashin tsarin kawo sauyi na shirin ayyukan noma na gwamnatin Nijeriya na ATASP1, da nufin bunkasa samar da amfanin gona na masara da shinkafa da kuma sauran hatsi da ake nomawa a cikin gida.