A yayin da ake shirye-shiryen gudanar da Babbar Sallah a Nijeriya, masu sayar da dabbobi ne ke kuka rashin ciniki a bana.
Gidan rediyon Muryar Nijeriya ya ruwaito cewa yawancin kasuwannin dabbobi sun kasance babu mutane sosai a wasu jihohin kasar irin su Kano.
A hirar da gidan rediyon ya yi da shugaban kungiyar dabboi ta Gandun Albasa a Jihar Kano, Alhaji Yusuf Ahmed ya bayyana cewa kasuwar ta cika mail da dabbobi daban-daban a kan farashi mai rahusa, amma babu masu saye.
Ya ce a baya a lokuta irin wannan kasuwar kan cika da masu hada-hada, amma yanzu sai dai mutane su je su taya dabbobin sais u tafi.
Kazalika rahotanni sun ce farashin dabbobi ya karu a bana fiye da bara, inda ragon da aka sayar naira 25,000 a bara ya koma naira 30,000 a bana.
Masu sharhi kan tattalin arziki na ganin hakan yana da nasaba da hauhawar farashi da ake ta samu akai-akai a kasar.