Farashin danyen mai a kasuwar duniya ya karu ranar Juma’a domin fatan da ake yi kan karin bukatar danyen mai da ake yi a China da kuma raunin da dala ke kara yi.
Da safiyar Juma’a dai an sayar da gangar danyen mai samfurin Brent kan dalar Amurka 75.80 maimakon dalar Amurka 75.67 da aka sayar da ita ranar Laraba.
Ita kuwa gangar danyen mai samfurin WTI an sayar da ita kan dalar Amurka 70.70 maimakon dalar Amurka 70.62 da aka sayar da gangarta a baya.
Fatan da ake yi cewa tattalin arzikin China zai sake farfadowa, wanda aka yi hasashen cewa zai sa danyen mai ya yi tsadar gaske, ya sake karuwa bisa ga irin yadda aka rarrage yawan kudin ruwa a kan bashi a kasar.
Akan rage yawan kudin ruwa akan bashi ne domin domin zuba jari a masana’antu ya karu sakamakon saukin bashi.
Kazalika mai din da matatun man China ke tacewa ya karu da kashi 15.4 cikin 100 idan aka kwatanta da man da suka tace a watan da ya gabata.
Manazarta na tsammanin bukatar mai a kasar da ta fi sayen danyen mai a duniya ta ci gaba da karuwa a rabin shekarar da ya saura.
Irin wadannan alkaluman suna kara fatan karuwar bukatar danyen man a China.
Ma’aunin dalar Amurka, wadda ke auna darajar dalar Amurka idan aka gwada da darajar kudade irin su Yen din Japan da fan din Birtaniya da dalar Canada da Krona din Sweeden da Franc din Switzerland, ya fadi zuwa 101.668 da safiyar Juma’a.
Wannan faduwar darajar dalar tana karawa wadanda ke amfani da wasu kudaden karfin sayen karin danyen mai, lamarin da ke dada yawan cinikin danyen man.
Tasirinsa a Nijeriya
Kasashe masu sayar da danyen mai irin su Nijeriya ka iya samun karin kudin shiga kan don wannan karin.
Sai dai kuma tashin farashin danyen mai ka iya kara kudin man fetur a gidajen mai saboda masu sayar da tataccen man fetur din abin da suka saya za su sayar.
Kasashe irin Nijeriya da suka koma tsarin ‘halin da kasuwa ta yi’ wajen tsayar da farashin man za su fuskanci tsadar fetur idan farashin danyen mai ya ci gaba da karuwa.
Kazalika za su ci moriyar araharta idan farashin danyen mai ya sauka a kasuwar duniya.