Gwamnatin Jamhuriyar Nijar ta ƙaddamar da wata masana'antar sarrafa rodi karkashin kamfanin samar da ƙarafa a Ilela da ke yankin jihar Tahoua na ƙasar a ranar Litinin 25 ga watan Nuwamba.
Ana sa ran masana'antar wadda aka gina ta hanyar zuba jarin kuɗin CFA biliyan biyu, za ta dinga samar da tan dubu 20 na rodi a duk shekara, tare da samar da guraben ayyukan yi ga matasan Nijar, kamar yadda Ministan Ciniki da Masana’antu na ƙasar, Mista Seydou Asman ya bayyana a yayin buɗe masana'antar.
Masana'antar na wakiltar wani gagarumin ci gaba a fannin tattalin arzikin Nijar wajen dogaro da kanta, a cewar Minista Asman, yana mai yaba wa kamfanin Niger Steel Group bisa ga manufofinsa da ke tafiya da tsarin shugabancin mulkin soja na ƙasar karkashin Birgediya Janar Abdourahamane Tiani.
“Samar da wannan masana'antar bai tsaya ga iya shaidar nuna dabaru da kuma jajircewarJanar Abdourahamane Tiani na ganin Nijar ta tsaya da kafafunta ba kawai, yana nuna irin himma da gwamnati ta sa a gaba wajen bunƙasa hanyoyin zuba jari da ci gaban masana’antu,” a cewar Minista Seydou.
Don ƙarfafa irin waɗannan ayyuka, gwamnatin Nijar ta aiwatar da wasu tsare-tsare kamar na baya-bayan nan, inda ta ba da umarnin hana fitar da tarkacen ƙarafa, tare da tabbatar da samar da muhimman albarkatun ƙasa don amfanin cikin gida.
Ministan ya kuma jaddada cewa, masana'antar wadda take da alhakin samar da tan ɗin roduna 20,000 a duk shekara za ta matukar rage dogaron da Nijar ke yi kan kayayyakin gine-ginen da ake shigowa da su daga kasashen waje tare da biyan buƙatun da ake samu daga fannin gine-gine a ƙasar.