Dorcas ta ce gudanar da rayuwa da hannu daya akwai wahalar gaske. Hoto: Dorcas Poba       

Daga Firmain Eric Mbadinga

Dorcas Poba 'yar kasar Dimokuradiyyar Jamhuriyar Congo ce wadda ayyukan fasahar da take yi da manhajar canvas suke jan hankalin mutane.

Kamar duk wani matashin wannan zamani, ita ma daliba ce mai fasaha da take daukar lokaci a kafofin sadarwa inda take baje-kolin ayyukanta na fasaha.

Yadda zane-zanen da Dorcas ke yi da hannu daya suke da kyau ne ya kara jawo hankalin mutane zuwa gare ta, ciki har da Uwargidan Shugaban Kasarsu, inda gidauniyarta ta dauki nauyin shirya wani bidiyo domin nuna ayyukanta.

A Kinshasa, inda take rayuwa, Dorcas ta bude wani dan karamin wajen aiki, inda a wajen ne take fitar da kayatattun ayyukanta.

Da hannunta na dama, matashiyar mai shekara 25 take aiki, inda take tsoma alburushi a cikin fenti da hannun, sannan ta yi zane da shi.

Bayan dogon nazari, wanda wasu lokutan yakan kai kwanaki, Dorcas tana zana mutane, dabbobi ko kuma wasu abubuwan da ke da alaka da yanayi.

A duk lokacin da take aiki, ba karamin abu ba ne yake dauke mata hankali. Sautin tsuntsuye da maganganun wadanda suke kusa da ita, sukan kara mata lissafin fitar aiki.

Dorcas ta yi amannar cewa nakasarta ce ta kara mata karfin gwiwa. Hoto: Dorcas Poba "Yanzu ina iya yin abubuwa da yawa ne.

Nakan fitar da abubuwa da yawa kafin in fitar da asalin abin da zan zana," in ji mai fasahar, wadda alamu suka nuna shiru-shiru ce a tattaunawarta da TRT Afrika.

Zane-zanen Dorcas suna nuna sha'awar da take yi wa yanayi da ayyukan fasaha.

Tun tana karama, matashiyar take sha'awar ayyukan fasaha, hakan ne ya ja hankalinta har ta shiga makarantar koyon aikin fasaha domin cika burinta.

Daga cikin fitattun ayyukanta akwai wani zanen wata mata da miji da suka bukaci ta zana su da alburushi domin su ajiye tarihi. Poba tana samun tallafin kudade daga fitattun mutane.

Dorcas tana da dimbin masoya a kafafen sadarwa. Hoto: Dorcas Poba 

A Gasar Cin Kofin Nahiyar Afirka da aka yi na karshe, Dorcas ta nuna kaunarta ga kasarta, inda ta zana damisa a gaban kofin gasar, sannan ta ratsa tutar kasarta a cikin zanen, sannan ta rika goyon bayan kasarta a gasar.

Tana da kusan mabiya 70,000 a TikTok, wannan dimbin masoyan ne da sauransu ne suke kara tallata ayyukanta ga masoya ayyukan fasaha.

"Babu dadi rayuwa da hannu daya, amma na riga na saba, sannan wannan nakasar na cikin abubuwan da suke kara min karfin gwiwa.

Da farko wasu mutanen suna kallon nakasar a matsayin fadawa a gare ni, amma na yi duk mai yiwuwa wajen mayar da nakasar ta kara min karfin gwiwa," in ji Dorcas.

Shigarta makarantar Kinshasha Academy of Fine Arts, inda yanzu take ajin karshe, ya sa Dorcas ta kara kwarewa a aikin.

"Na taso ne na wayi gari ina zane, ban ga wata dangantaka da ke tsakanin nakasata da abin da nake sha'awa ba."

Dorcas Poba

"Mutane da dama suna min kallon abar koyi. Amma zama abar koyi ga wasu na da nauyi domin wasu lokutan nakan yi kuskure a aikin, duk da cewa asali aiki ne na masu hannu biyu.

Akwai lokutan da nake kasa fitar da abin da ke cikin raina a zane," inji ta, kafin ta kara wa kanta karfin gwiwa.

"Abin da ke kara min karfin gwiwa shi ne tuna gwargwarmayar da na sha a baya, domin na sha yanke kauna a baya. Nakan ji kamar ba zan iya ba, ko ya kamata in daina aikin nan."

"Amma idan na ga yanayin duniyar da muke rayuwa, sannan na kuma ga nasarar da na samu, nakan kara kara samun karfin gwiwa."

Burin Dorcas yanzu shi ne ya bude shagon koyar da matasan kasar Dimokuradiyyar Jamhuriyar Congo zane-zane.

Wannan burin ne ya sa take ta kara kaimi wajen cigaba da ayyukan fasahar.

TRT Afrika