Daga Kudra Maliro
Jamhuriyar Dimokuradiyyar Congo ta sha fama da munanan tashe-tashen hankula na tsawon shekaru, yanayin da ya haifar da babbar barazana ga lafiyar kwakwalwar mutane musamman mata da yara.
Kasereka Kasolene, wani matashi dan wasan rawa ya samar da mafita ta musamman.
Yana amfani da basira da hikimarsa ta rawa don bai wa mutane damar samun nutsuwa da kwanciyar hankali sakamakon rikice-rikicen da kasar ke fama da su.
Kwararren dan wasan mai shekara 23 ya fara kwaikwayon fitattun jaruman Amurka irinsu Michael Jackson da Chris Brown tun yana dan shekara takwas.
"Na fara sana'ar rawa tun a shekarar 2016. An zabe ni na karanci rawar gargajiya da ta zamani a Ecole Sables da ke Senegal na tsawon shekaru uku," kamar yadda ya shaida wa TRT Afrika.
Kasolene da kungiyarsa na yunkurin isar da sakon zaman lafiya ta hanyar rawa a birnin Goma da ke gabashin DRC.
Suna wasanni a wuraren da jama'a suka taru kamar kasuwanni da kan tituna don nishadantar da wayar da kan al'ummar da rikicin ya rutsa da su a yankin da ake ci gaba da jin kararrakin bindigogi da sauran makamai.
Gamsuwa da Samun da nutsuwa
Kungiyar rawa ta Inuka ta hada gomman matasa wadanda ke amfani da hikimarsu ta rawa a matsayin wani nau’i na ba da magani.
“Idan muka ware lokutanmu na rawa tare da yaran da ke cikin damuwa, sai su manta, domin rawar na taimaka musu shawo kan bacin rai da suke ciki tare da taimaka musu yin tunani kan wani abu daban maimakon bala'o'in da sukagani a lokutan tashe-tashen hankula na kasar, musamman wadanda suka fito daga Arewacin Kivu,” a cewar Abdoul Tambwe daya daga cikin ’yan rawa na kungiyar Inuka.
"Godiya ta musamman ga wannan bangare da kungiyar Inuka ta ware, yara suna samun damar sanin junansu da kuma sanin halin da suka fada ciki. Ta hanyar rawa, suna bayyana yadda suke ji ta hanyar wasa da hikima.
Kungiyar rawar tana ba su damar fitar da duk wata damuwa da ke jikinsu tare da ba su damar motsa jikinsu,”in ji shi.
“Bangaren rawar da muke yi na taimaka wa yara samun sauki. Yana taimaka wa wajen ba su kwarin gwiwa da kuma sanin kimar kansu, domin su ne shugabannin Kongo na gaba,” a cewar Mista Tambwe.
"A matsayina na dan’wasa, aikina shi ne na taimaka wajen wayar da kan jama'armu tare da ba su kwarin gwiwa don mu kauce wa rikice-rikicen da ake samu tsakanin al'ummomi da ke janyo asarar rayukan mutane da dama," in ji shi.
Rawa babu iyaka
Dakarun Congo da kawayenta sun shafe watanni suna kai farmaki a gabashin Jamhuriyar Dimokuradiyyar Congo a kokarinsu na fatattakar 'yan tawayen kungiyar M23 daga yankin.
Dubban mutane ne rikicin ya raba da muhallansu inda suke zaune a sansanonin da ke kusa da birnin Goma.
Ga Kasolene, nishadi ba shi da iyaka. Yana mai ba da tabbacin cewa ba shi da wata matsala da sauran kasashe duk da sabanin da ke tsakaninsu da DRC.
A halin yanzu Kasolene na halartar wani bikin rawa da ke gudana a Goma tare da wasu kungiyoyin ’yan rawa da dama da suka fito daga kasashen Rwanda da Burundi da kuma wasu kasashen da ke makwabtaka da DRC.
Ana sa ran bikin zai taimaka wajen inganta hanyoyin zaman lafiya a tsakanin mutanen yankin da kuma rage tashe-tashen hankula da ake fuskanta.
"Muna so mu nuna wa duniya cewa DRC da Rwanda kasashe biyu ne da ke 'yan uwantaka da abokantaka da juna," a cewar Mista Batumike, wanda ya shirya bikin rawar a Goma.
Ya yi bayanin cewa ’yan wasan Rwanda da Kongo sun shafe fiye da mako guda tare a Goma, suna yin atisaye a wuri daya.
Kasolene da kungiyarsa na shirin kai ziyara sansanonin 'yan gudun hijira da ke kusa da Goma don koyar da rawa da kuma taimaka wa mutanen da suka rasa matsugunansu samun shawo kan matsalolin da damuwa da suka shafi rikici.
"Manufar ita ce a hana yaran da ke zaune a wadannan sansanonin su fada kan titi, idan suka kware a rawa, za su iya kula da kansu," in ji shi.
"Muna kokarin bayyana hoton DRC ta hanyar rawa kuma muna fatan cewa nan da 'yan watanni ba za mu dinga magana kan rikicin yankin Gabashin Kongo ba, baya ga abubuwan al'ajabi da yankin ke bayarwa.
"Mu ‘yan wasa ne kuma masu ba da ilimi ga al’umma,” in ji Mista Kasolene.