A daidai lokacin da adadin dabbar karkanda ke raguwa, gandun dabbobi na Jamhuriyyar Dimokradiyyar Kongo ya kara samun habaka.
An kai karkanda 16 na kudanci cikin gandun – wanda hakan ya kara yawan karkandan da ke cikin gandun.
Karkanda na daga cikin dabbobin da ke kara fuskantar barazana daga masu farauta ba bisa ka’ida ba.
An kashe farin karkanda na karshe da ke gandun dabbobin Garamba da ke arewa maso gabashin Jamhuriyyar Dimokradiyyar Kongo, a 2006, inda gandun ya zama babu karkanda ko guda.
Sai dai a halin yanzu an kara samun kwarin gwiwa.
A wata sanarwar hadin gwiwa da aka fitar ranar Asabar, hukumar gandun dajin garamba ta bayyana cewa akwai fararen karkanda 16 da aka dauke su daga Kwa-Zulu Natal da ke Afirka ta Kudu zuwa arewa maso gabashin Kongo.
Jin dadi da sa rai
“Dawowar fararen karkanda Jamhuriyyar Dimokradiyyar Kongo ya nuna yadda kasarmu ke bayar da muhimmanci kan kiyaye dabbobi,” in ji Yves Milan Ngangay, darakta janar na cibiyar nazari kan kiyaye muhalli da gandun daji.
Kungiya mai zaman kanta mai kula da gandun dabbobi ta ICCN da kamfanin hakar ma’adinai na kasar Canada na Barrick Gold ne suka dauki nauyin wannan aikin.
Wani bidiyo da kungiyar ta African Parks ta yi, an nuna masu gadin gandun suna sakin fararen karkandan cikin Gandun Dabbobin Garamba sa’o’i bayan sun isa daga Afirka ta Kudu.
“Mun ji dadi da muka sake ganin irin wadannan nau’in na dabbobi a gandunmu na Garamba kuma muna sa ran masu yawon bude ido daga duka fadin duniya za su ci gaba da kawo ziyara yankin mu,” in ji Maguy Nabintu wanda ma’aikaci ne da kamfanin Barrick Gold wanda yana nan lokacin da aka kai karkandan.
“Akwai bukatar mu taimaka wa ma’aikatan gandun daji domin mu kula da tsirrai da dabbobinmu,” kamar yadda Ms Nabintu ta shaida wa TRT Afrika.
An kafa gandun dabbobi na Garamba a 1938 kuma yana daga cikin gandun dabbobi mafi tsufa a Afirka.
Amma rikici da farauta ba bisa ka’ida ba da tsananin rashin tsaro a Kongo sun matukar kawo cikas ga dabbobin daji a tsawon shekaru.
Maye gurbi
Matsala ce da ba a DRC ta tsaya ba. Kamar yadda gidauniyar duniya kan gandun dji ta nuna, “tun da farkon karni na 20, karkanda 500,000 suke shawagi a Afirka da Asia.
Zuwa 1970, adadin karkandan ya ragu zuwa 70,000 kuma a yau, kusan karkanda 27,000 suka rage a duniya baki daya.”
Ganin cewa ana sa ran kai karin karkanda gandun dabbobi na Garamba nan gaba, masu sharhi sun ce akwai bukatar a dauki matakai domin magance matsalar ta farauta ba bisa ka’ida ba.
Masu farauta ba bisa ka’ida ba akasari sun far wa dabbobin daji domin samun sassan jikinsu wadanda ba wai ana amfani da su a cikin gida ba, ana sayar da su.
Suna da amfani wurin sarrafa kayan abinci da kayan shafe-shafe da kuma magungunan gargajiya da na zamani.
Sauran abubuwan da bil adama suke yi kamar sare itatuwa da kona dazuka sun lalata muhallan dabbobi.
Shugaban kungiyar African Parks, Peter Fearnhead ya ce kokarin da ake yi domin ceto fararen karkanda a gandun dabbobi na Garamba ya yi kadan kuma an yi jinkiri.
Sai dai ya ce yana da yakinin cewa sake kawo karkandan da aka yi “shi ne farkon mataki wanda fararen kankanda za su maye gurbin fararen karkandan da ke arewaci.”