Daga Emmanuel Onyango
An fara mayar da wasu nau'in bareyi da ba kasafai ake samu ba kasarsu, waɗanda aka ajiye su a gidajen namun dajin Amurka tsawon shekaru, wadanda aka yi amanna adadinsu a cikin daji bai wuce 100 ba.
Nau'in barewar mai suna mountain bongo da Turanci, ko kuma barewar tsauni, wani nau'in dabba ce da take ƙarewa wadda aka fara samu a tsakiyar Kenya kawai.
Su ne nau'in bareyi na uku mafi girma a duniya kuma ana iya bambance su da gashinsu mai ja-ja-ja-jaja da ratsin fari a tsaye.
An mayar da da yawansu Amurka daga Kenya a shekarun 1960 a karkashin wani shiri da gwamnatin mulkin mallaka ta Burtaniya ta yi.
Haka kuma an kai wasu bareyin zuwa Turai, yayin da ‘yan mulkin mallaka ke wawashe dukiyar Afirka.

Dabbobin da ake kai wa Kenya zuriyar wadanda Turawan mulkin mallaka suka yi safararsu ne. Sai dai masu rajin kare muhalli sun ce matakin na baya bayan nan zai taimaka matuka wajen kiyaye nau'in dabbar.
“Wannan matakin ya cece mu a zahiri saboda ba mu da sauran irin su da suka rage a nau'insu. A yanzu muna iya neman su ba mu abin da suke da shi a wurin,” kamar yadda mai magana da yawun Hukumar Kula da namun daji ta Kenya Paul Udoto ya shaida wa TRT Afrika.
"Abokan hulɗarmu a Amurka sun zaɓi tsara dawowar su."
Sabbin rukunin bongo da aka mayar da su Kenya daga Amurka ranar Lahadi ƙarƙashin gidauniyar Rare Species Conservatory Foundation (RSCF), 17 ne da suka haɗa da (mata 12 da maza 5).
Yana daga cikin yunƙurin da ƙasar ta Gabashin Afirka ke ci gaba da yi na haɓaka yawan dabbar a cikin gida.
Manufar ita ce a kara yawan dabbobin zuwa 750 nan da shekaru 50 masu zuwa, in ji Darakta Janar na Hukumar Kula da Daji ta Kenya Erustus Kanga, kamar yadda ya shaida wa manema labarai yayin da ake sauke wasu katafaren kejin katako dauke da dabbobin daga wani jirgin dakon kaya a babban filin jirgin saman kasar da ke Nairobi babban birnin kasar.

"A cikin watanni uku masu zuwa ya kamata mu samu mutane biyar daga wasu gidajen namun daji a Turai su zo su kawo wasu nau'ikan kwayoyin halitta domin mu bunkasa yawan dabbobin nan," in ji shi.
Ya kara da cewa "Idan aka ba mu dama da goyon baya za mu dawo da dukkan bareyin bongo na tsaunuka da ke wajensu."
Za a ajiye dabbobin a wani keɓaɓɓen wuri na akalla watanni uku don sa ido sosai tare da sanin yanayin da suke ciki kafin a sake su a cikin daji, in ji jami'ai.
An ci gaba da yin kiwo da sake farfado da nau'in bareyin a wurin zamansu na ainihi a Tsaunin Kenya, wanda shi ne mafi tsayi a ƙasar.

Ministar kula da yawon bude ido ta Kenya Rebecca Miano ta ce bareyin tsauni na bongo "sun shafe shekaru suna cikin takura da uƙuba,"
“Daga asarar matsuguni zuwa farautarsu da fama da cututtuka, sun sa yawan bareyin bongo ya ragu sosai. Amma duk da haka, ko da a cikin wannan halin da ake ciki, mun bijire wa durkusar da matsin lamba don sakin wannan fitaccen nau’in,” in ji ta.