Grammys: Rocky Dawuni na Ghana na daga wadanda suka fi iya kwalliya

Grammys: Rocky Dawuni na Ghana na daga wadanda suka fi iya kwalliya

An yana wa kayan Dawuni da cewa suna da kayatarwa da kyawun da ya gada gashajiya da zamani.
Ghanaian reggae star Rocky Dawuni

Daga Pauline Odhiambo

Mawakin zamani dan kasar Ghana Rocky Dawuni ya kusa rasa wani matsayi a wajen Gasar Mawaka Mafiya Kyau ta Grammy karo na 66, amma a karshe ya samu kambin tufafin da ya fi kayatarwa.

Mawakin na Ghana da samar da ‘In Ghana’ ya samu matsayin ne bayan bayyana a Munallar Esquire inda tare da sauran mawaka ya shiga jerin wadanda suturarsu ta maza ta fi kyau da kayatarwa.

Esquire mujallar maza ce a Amurka da aka sani da mayar da bankali kan tufafi. A wajen bikin, an yaba wa kayan Dawuni da cewa suna da kayatarwa da kyawun da ya gada gashajiya da zamani.

Kamannin al’ada

Gashin bakinsa tare da kayansa masu kalar hauren giwa da aka samar a Ghana na bayyana kamanni da yadda al’adarsa take wanda su suka ja hankali a minbarin taron.

“Wadannan ne gayun da suka nuna sun shirya su sanya masana’antarsu yin alfahari, taimaka wa garin da aka daidaita, tare da tabbatar da har ma masu kallon daga gefe za su tuna me ya sa muke kallon wakoki ma,” in ji mujallar a wani sako da ta fitar a shafinta tare da hoton Dawuni da sauran mawaka, inda take bayar da misali da annobar gobarar da ta faru a Los Angelos da ta shafi jaruman Hollywood da dama.

An saka sunan Dawuni a manyan maaaka na duniya da aka fi yaba musu, cikin su har da Busta Rhymes, John Legend, Omarion, da Swizz Beatz da ma sairan su.

Ga dai manyan mawakan Afirka da flsuka fito a munallar ta Esquire:Trevor Noah Wannan ne karo na biyar da yake karbar bakuncin Grammy, dan wasan barkwancin na Afirka ta Kudi ya bayyana a wajen taron da kayan Giorgio Armani da takalmin Christian Louboutin.

Tsohon mai gabatar da shirin Daily Show dan shekara 41 ya kuma sanya wani bajon ado na daham da kanfanin Tiffany & Co suka samar.

Lojay

Mawaki kuma mai rubuta waka dan Nijeriya da ya yi shuhura da wakar Monalisa, ya saka rigar suit a wajen taron na Grammy’s.

Mawakin dan shekara 28 ya yi ado da zoben zinare da azurfa da sarkar da ta dace da su.

Shaboozey

Mawaki dan asalin Nijeriya kuma Ba’amurke, Shaboozey ya shiga wajen taron a wata rigar fiit launkn azurfa da baki da kamfanin Jacob & Co suka samar.

Mawakin ya samu shuhura ne bayan ya fito a wakoki biyu a album din Beyonce na 2024 wato rukunin wakokin ‘Cowboy Carter’ da ya samu lashe kambin Kasa Mafi Kayatarwa a 2025 Grammy’s.

Kayan da Shaboozey ya saka tare da abin wiya da zobe na gani na fada sun ja hankali sosai a wajen taron.

Sauran shahararrun mawaka da suka samu kambin tufafi mafi kyau na Mujallar Esquire sun sada da Cory Henry, mawakin jazz da bible kuma DJ na Amurka da Mustard da ke nasar wakoki.

Henry da ya sanya kayan suit farare fat, ya tafi gida da kambin Wakokin Buble Mfiya Kyau, ina da Mustard kuma da ya sanya wata riga mai jan hankali da kalolinta da yawa, ya samu kambin Mawakin Gambara Mafi Kayatarwa.

TRT Afrika