Daga Dayo Yussuf
Jailosi yana tashi kowace rana da safe don ya bude shagonsa a hanyar wata kasuwa mai suna Kariokor a birnin Der es Salaam kuma daga nan ne yake fara sana'arsa. Yana yin takalma ne sai dai ba kowane irin takalmami hadawa ba.
Jailosi ya kware wajen yin takalman sandal da ake kira da Masandale wanda ake samarwa daga tsofaffin tayoyin ababen hawa.
"Ana son wadannan sandal din a birnin Arusha. Yanzu kuma bukatarsu ta yadu zuwa sauran biranen kamar Iringa da Dodoma da kuma Mbeya," kamar yadda ya shaida wa TRT Afrika.
Jailosi yana amfani da wata wuka mai kaifi sosai wajen yanka tayar daga nan kuma sai ya fitar da siffar da yake so. Ya kwashe lokaci mai tsawo yana wannan aiki.
Kuma ba ya amfani da abin da ke fitar da siffar takalmi don samun irin siffar da yake so. Yana cin baki-bakin takalmin ne cikin sauri, ba tare da bata wani lokaci ba, sai ka ga an kammala hada sandal.
"Ina kwashe akalla minti 15 zuwa 20 kafin na kammala hada takalmi kafa biyu," in ji Jailosi.
Biyan bukata da sauki
'Yan kabilar Maasai suna son sandal din – kabilar tana zaune ne a kasashen Kenya da Tanzaniya. Saboda kwarinsa sauran al'ummu na Kenya kamar Kamba da Kikuyu su ma suna amfani da shi a matsayin kayan al'adarsu. Daga kallon yadda aka yi takalmin mutum zai iya gane kabilar da ke amfani da irinsa.
Jailosi ya fara yin takalmin Masandale bayan ganin irin tarin tayoyin da aka jibge, ba a amfani da su saboda babu wanda ya san abin da za a yi da su. "Ni ina kallonsu a matsayin wata hanyar samun kudi," kamar yadda ya shaida wa TRT Afrika.
“Mutane da dama sun zabi su yi amfani da wadannan takalman saboda suna da juriyi ba kamar takalman zamanin ba," in ji shi. "Za ka iya amfani da shi tsawon shekaru."
'Yan mitoci kadan daga shagon Jailosi, Romani shi ma yana yin irin sandal din. Yana samun kudi, amma ya ce yana jin dadi idan ya tuna cewa yana amfani da tsofaffin tayoyin da ake amfani da su ne ta hanyar da ta dace.
"Duk inda ka je za ka ga tarin tayoyin a jibge. Mutane sun yi amfani da su kuma sun watsar da su. Babu wani abu da za a iya yi da su. Saboda haka ya kamata mu yi takalma da su," in ji Romani.
Tsaunin tsofaffin tayoyi
Tanzaniya, kamar sauran kasashen Afirka, tana fama da matsalar da tsofaffin taya (wadanda aka daina amfani da su) ke jawowa ga muhalli.
A shekarar 2016, gwamnati ta yi wata doka mai tsauri wadda ta haramta shigo da tsofaffin tayoyi. Kazalika dokar ta hana shigowa da tayoyi da dangoginsu da suka wuce shekara takwas da yi.
Wannan ya jawo raguwar yawan tsofaffin tayoyin da ake zubarwa a matsayin shara, sai dai masana suna cewa da sauran matsala.
Ellen Otaru, shugabar wata Kungiyar 'yan jarida masu kare muhalli ta the Journalism Environmental Association, ta shaida wa TRT Afrika cewa babu isassun bayanai don daukar matakin da ya dace.
"Ba ma yin bincike da nazarin da ya dace kan abin da ya kamata a yi da tsofaffin tayoyin da aka daina amfani da su da kuma yadda hakan yake tasiri ga muhalli da rayuwa gaba daya. Babu wanda yake sanya ido kan yadda ya dace a tafiyar da shara."
A Tanzaniya, ya zama ruwan dare ka ga ana kona tarin tayoyin da ke fitar da bakin hayaki mai kawo gurbatacciyar iska a sararin sama.
Taya ba ta rubewa kuma tana kwashe shekaru masu tsawo a karkashin kasa. Kodayake ana bukatar a sake yin nazari, amma masana na cewa taya tana fitar da sinadarai masu guba ko da ba a kona ta ba.
A yanzu a kowace shekara ana samun tayoyi fiye da biliyan daya a duniya. Maimakon a samar da hanyar sarrafa su ba tare da jawo illa ga muhalli ba, amma sai kasashen da suka ci gaba su turo su wasu kasashe.
"A wasu kasashe da suka ci gaba kamar Canada, suna amfani da tsofaffin tayoyi ne wajen samar da mai. Sai dai har yanzu ba a fara yin haka ba a nahiyar Afirka saboda abu da ake kashe kudi sosai," in ji Ellen.
"Wasu kasashe suna turo tsofaffin tayoyin su ne zuwa wasu kasashe masu tasowa, amma babu wani da zai sanya ido kan yadda ake amfani da su."
A Afirka, galibin wadannan tayoyi da aka daina amfani da su ana kona su ne. Masana kiwon lafiya suna gargadi kan hayakin da hakan hadarin hakan saboda sinadarai masu gurbata muhalli kamar cyanide da carbon monoxide da kuma sulphur dioxide da kona tayar ke jawowa.
An gano hanyar magance matsalar
Labari mai dadin shi ne mai yin takalmin sandal kamar Jailosi ya samar da hanyar sake amfani da tsofaffin tayoyi wadanda ba su da kyan gani.
"Akwai matasa da dama da suke sake amfani da tayoyin wajen shuke-shuke da gyaran lambu da takalma da kuma gine-ginen bandakuna," in ji Ellen.
"Amma ya kamata a kara fadada wadannan aikace-aikacen a matakin gwamnati ko kuma nahiya saboda ya yi tasiri sosai."
Yayin da aka ci gaba da yin bincike kan yadda za a yi da tsofaffin taya ko kuma a samu wani da za a maye gurbin taya da shi, mutane kamar su Jailosi da Romani za su ci gaba da bayar da karamar gudunmawa wajen kare muhalli, gara a rika maganin matsalar da kadan-kadan.