Kabilar Makonde da ke Tanzania ta yi fice sakamakon al’adunta da tarihi da fasaha.
Duk da cewa al’adar da suke da ita ta sassaka na gushewa a shekarun da suka gabata, amma wasu masu aikin sassakar kamar Sebastian Daniel Mbebe na kokarin farfado da aikin – domin jama’ar Afirka.
Mbebe ya gaji wannan aiki daga mahaifinsa da kakansa. “Ayyukan da nake yi sun fi mayar da hankali kan fasahar yau da kullum.
Na samu dangina a cikin wannan al’ada. Ta hakan na zama mai sassaka. Na soma ne da kananan abubuwa har zuwa lokacin da na girma,” kamar yadda ya shaida wa TRT Afrika.
Soyayyar sassaka
Yana amfani da da fasaharsa domin bayar da labarin Afirka, da alkinta al’ada da kuma kara jawo masu yawon bude ido.
“Yana daga cikin al’adar kabilar Makonde,” kamar yadda mai sassakar ya bayyana.
Sassaka na daga cikin al’ada da tarihin Afirka mafi girma. Sebastian Mbebe na amfani da katako domin sassaka iri daban-daban – ba laka ba karfe.
“Ba mu amfani da laka. Muna amfani da itace, kowane irin ice, amma akasari muna amfani da bakin katako na Afirka wato Mpingo, saboda yana da kwari kuma yana dadewa tsawon lokaci.
Amma sassaka na da sauki,” in ji shi. A daidai lokacin da yake kokarin ceto fasahar da ke kokarin gushewa, Mbebe na ganin akwai bukatar ‘yan Afirka su yi kokarin farfadowa da kuma nuna soyayyarsu ga fasahar gargajiya.
“Ga kasuwar cikin gida, muna bayar da kwarin gwiwa ga ‘yan Tanzania da kuma ‘yan Afirka baki daya da su so fasaha. Sai dai mafi yawanci mun fi dogara ne kan ‘yan kasuwa daga waje,” in ji shi.
Aiki mai wahala
Wannan aikin na bukatar dabarun sana’a sosai da kuma hakuri saboda masu sassaka har yanzu ba su amfani da kayayyaki na zamani.
Ana shafe wata kafin a sassaka wani abu da zai ja hankalin mutanen gida da baki daga kasar waje.
“Misali,” Ujamaa” na da tsawon kafa shida. Hakan na nufin idan aka yi aiki a kanta a kullum, za a iya daukar watanni uku zuwa hudu sakamakon muhalli da kuma kayayyakin aikin da ake amfani da su,” kamar yadda Mbebe ya kara da cewa.
Yana yin sassake-sassake daban-daban domin nuna rayuwa da kuma al’adar Afirka.
“Wata mahaifiya tana hanyar zuwa gona, tana dauke da abubuwa, akwai kuma abubuwan da muke amfani da su, kamar rariya da galma,” kamar yadda ya ce.
“Zai iya yiwuwa sassakar ta nuna mahaifiya ce ke girki a yayin da take kallon wani, tana gaya masa ‘ka da ka je wurin, ina girka abinci,’ irin dai wadannan abubuwan.
Akasari, ba mu nuna al’adarmu ta Afirka, musamman wata kabila,” kamar yadda Mbebe ya kara da cewa.
Duk da cewa mai sassakar na Tanzania na da burin alkinta al’adun Afirka, amma ya dauki aikin da yake yi a matsayin kasuwanci domin kula da iyalinsa daga ciki har da tura ‘ya’yansa makaranta.
Annobar korona ta yi matukar illa ga tattalin arzikin duniya. Haka kuma wannan lamarin ya shafi batun sassakar da yake yi.
Amma Mbebe ya ce abubuwa suna kara gyaruwa. “Ba mu kammala dawo daidai ta bangaren kudi ba.
Ita ma kasuwarmu ba ta samu daidaito ba, ko yadda kwastamominmu ke zuwa kafin korona ya sha bamban.
Babu asara
Bayan korona, ana kara samun kalubale, amma ba mu bari ba. Muna ci gaba da aiki.
Muna samun riba saboda muna samun kudi kadan, yara na zuwa makaranta, ana ci gaba da rayuwa, kuma mun gode wa Ubangiji.”
ba shi nishadi sakamakon tasirinta a tattalin arziki da al’ada.
“Kwarin gwiwata na zuwa ne daga fasaha. Idan ana maganar riba, eh muna samun riba, amma babu wata asara a duk wani aiki idan kana yin shi kullum.”