Wani mai tallan kayan kawa namiji, mai tsawon kafa shida, yana tafiya yana kallo, hannayensa a bude, kuma idanunsa a bude ba tare da kifta su ba duk da cewa akwai hasken kyamarorin masu daukar hoto.
Takun mai tallan kayan kawan suna daukar hankali, kodayake adon da aka yi a gaban rigarsa ce ke jan hankalin jama'a.
Riga 'yar-ciki, riga ce da ta samu asali daga arewacin Nijeriya, wadda ake yi wa aikin hannu da ta samu karbuwa a wurare da dama.
Wasu sauran suturun da aka baje-kolinsu a wannan rana suna kama da juna: suturu ne da aka yi wa ado da salo na musamman.
Salo da babu irinsa
‘’Na dade ina sha'awar ado da kwalliya. Abu ne da na dauka da muhimmanci kuma saboda haka ne na kafa wannan cibiya, inda ado da kwalliya suke hadaway," kamar yadda Austin Aimankhu wanda ya shirya bikin baje-kolin, ya shaida wa TRT Afrika.
Kusan tsawon shekara tara, Aimankhu yana samar da abin da yake kira 'kayayyaki kwalliya', wadanda suke sake fasalin ado da kwalliya daga kyallaye kanana da ake dinka su don su samar da wani gagarumin adon Afirka da kuma al'adarta.
"A cikin kaina, ina son mutane su rungumi salon tufafin Afirka. Hanya ce babba ta bunkasa muryar Afirka a fagen ado da kwalliya na duniya," in ji shi.
‘’Ina da digiri a fannin shari'a amma ban taba yin aikin lauya ba. Na yi karatun fannin lauya ne saboda nuna wa mutane za ka iya zama duk wani abu da kake so, amma ina matukar kaunar kwalliya da al'ada.
"Na shiga fannin ado da kwalliya ne a shekarar 2000, amma bayan fiye da shekara 10 na aikace-aikacen al'adu, sai na fahimci akwai bukatar na kara kaimi."
Bunkasa ado da kwalliya
A shekarar 2014, Aimankhu ya kaddamar wani shirin ado da kwalliya wanda ya yi suna da 'shirin sanya kayan 'yan Nijeriya.'
Kowanne daga cikin tufafin an yi mai aikin hannu ne.
‘’Ina amfani da abubuwa kamar corals da weaves da sauransu, kai duk wani da ya zo raina da zai kara wa abin armashi. Wannan ne kalaman da yake yawan fada."
Aimankhu yana aiki da masu kirkire-kirkire ciki har da tailoli da masu zane-zane.
‘’Kirkire-kirkire yana daukar sa'o'i ko kuma kwanaki. Yi wa wasu kayayyaki ado da launi zai iya daukar tsawon wata uku.
Ni ne daraktan kirkire-kirkire, kuma ni ne nake fara matakin farko na aikin da zane-zanen farko, daga nan ne ake bunkasa aikin da kuma yin aikin hannu."
Al'adar Afirka
Afirka tana da dadadden tarihi sutura da ya dogara sosai a kan zayyane-zayyane.
Sutura mai adon kamfala na yammacin Afirka su ma manyan misalai ne. Wadannan sutura za a iya nunka su ko lankwasa su kafin a kulle su, sannan a saka su cikin ruwan rini.
Sakamakon wannan aiki shi ne damar da launuka iri-iri da masu aikin suke kira da "tambarin Afirka," nahiya mai launuka. Amma kamar sauran kayayyakin al'adun Afirka, abubuwa suna sauyawa kadan.
‘’Ka taba ganin ado iri-iri a taron kawa? Ya yi kama da wanda ake gani a birnin Milan. Sannu a hankali mun fara rasa abubuwan da suka sa muka zama 'yan Afirka," in ji Aimankhu.
‘’Suturata tana tuna mana da dimbin salon ado da kwalliyar Afirka," in ji shi.
Matan karkara
‘’Kayanmu suna da muhimmanci sosai wajen fada wa duniya labarinmu. Kalli yadda Indonesiya ta sa salon tufafin batik ya samu karbuwa. Wannan ne abin da ya kamata mu rika yi da suturunmu," in ji shi.
Aimankhu ya fadada tsarin baje-kolinsa ta hanyar amfani da fasaha don inganta salon aikinsa.
‘’Na bunkasa sana'ata ta hanyar fasaha, wanda take taimakawa wajen tabbatar da cewa kaya ba sa zuba, sai dai ba haka batun yake ba wajen matan karkara wadanda suke rinin kamfalarsu a gida."
Shekaru masu zuwa
Aimankhu ya yi amanna cewa akwai abubuwan da za a amfana da su idan suturun Afirka suka ci gaba da samun karbuwa a duniya. "Idan muka iya rina kayan Afirka ba tare da sun yi zuba ba, hakan zai sa a rika son kayanmu a kasuwanni kayan ado da kwalliya na duniya."
Yanzu Aimankhu yana aiki a fannonin al'adu da ado da kwalliya a fadin nahiyar.
Ya gudanar da taruka kuma yana yawan magana kan muhimmancin hade bangaren ado da kwalliya waje guda don alkinta al'adun Afirka.
‘’Abu da ya kamata a koya wa 'yan baya. Don su fahimci kyau ado da kwalliyar Afirka a suturan 'yan Afirka," in ji shi.