Dalilin da ya sa aka haramta wa maza yin kitso a Zanzibar

Dalilin da ya sa aka haramta wa maza yin kitso a Zanzibar

Zanzibar ta soma aiwatar da wata doka mai tsauri wadda ta haramta wa maza yin kitso.
Gwamnatin Zanzibar ta ce maza su yi kitso ya saba wa al'ada. Hoto/Getty Images

Daga Charles Mgbolu

Yadda curin tsibiran da ke Zanzibar da ke Gabashin Afirka suke, na kawatar da idanu da kuma jawo masu yawon bude ido.

Hotunan tsibiran daga saman jirgi na nuna yadda Tekun India ya zagaye duwatsu da kuma bakin teku mai kyan gani ga kuma itatuwan kwakwa da suka dan kwanta wadanda ke kada iska inda suke maraba da baki.

Sai dai Zanzibar ta zama abin da ake tattaunawa a shafukan sada zumunta saboda wani dalili na daban. Gwamnati ta soma aiwatar da dokar haramci ga maza su yi kitso, inda wadanda suka saba dokar za su iya biyan tarar sama da dala 400 ko kuma zama gidan yari na wata shida ko kuma duka biyun.

Bakin tekun Zanzibar wuri ne da masu yawon bude ido ke son zuwa. Hoto/AA

Dokar wadda dama akwai ta tun a 2015, ba a tsaurara ta ba tun a baya. Babban sakataren hukumar kimiyya da fina-finai da al’adu ta Zanzibar, Dakta Omar Adam ya shaida wa manema labarai na kasar cewa an dauki matakin ne domin kare gargajiya da kuma al’adun mutanen kasar.

“Ya rage naku ko dai ku biya tara ko kuma ku sayi reza ku yi aski,” kamar yadda Omar ya shaida wa manema labarai.

“Muna ganin lamari ne mai hatsari ga ‘ya’yanmu masu tasowa. Wannan wani nau’i ne na rashin da’a a Zanzibar kuma al’ada ce wadda aka dauko daga wajen Zanzibar,” kamar yadda Omar ya kara da cewa.

“Babban cin zalin yara maza da manya a Zanzibar! Iko da gyaran gashin mutane?” kamar yadda wani mai amfani da shafin Twitter @slevyDC ya bayyana.

“Kasashen Afirka na tsayawa kan manufarsu a maimakon na kasashen yamma,” kamar yadda @GlamParte a shafin Twitter ya goyi bayan matakin.

Sai dai babbar damuwar ta fito ne daga mazauna kasashen waje, sakamakon Zanzibar na daga cikin manyan wuraren zuwa ga masu yawon bude ido a Afirka.

Zanzibar wuri ne na yawon bude ido a Afirka. Hoto/AA

Wani mai zagayawa da masu yawon bude ido JM ya bayyana cewa akwai masu son zuwa yawon bude ido da ke ta tura masa sakonni suna neman karin bayani kan idan wannan sabuwar doka ta shafi baki daga kasashen waje.

“Tarar ba ita ce ta dame su ba. Sai dai fargabar su ita ce za a iya kama su, kuma ba wannan bane abin da ke a cikin ranka idan za ka je hutu,” kamar yadda ya shaida wa TRT Afrika.

Rashin tabbas kan yadda ya shafi ‘yan kasashen waje ya kara jawo labaran karya a kafofin sada zumunta, wanda hakan ya sa ministar watsa labarai da al’adu da matasa da wasanni, Tabia Maulid Mwita ta yi jawabi ga manema labarai.

Ta yi karin haske inda ta bayyana cewa wannan dokar ta tsaya ne kan matasan Zanzibar, kuma Zanzibar din tana girmama diflomasiyya da al’adun sauran jama’a.

“Ba za mu iya hana mutane daga wajen Zanzibar yin al’adunsu ba,” kamar yadda ta bayyana.

TRT Afrika