Daga Pauline Odhiambo
Idan akwai wani abu da yake haɗa kan ƴan Nijeriya waje guda bayan ƙaunar da suke yi wa waƙa, da abinci mai kyau da kuma zaulayar ƴan Ghana da Afrika ta Kudu, to shi ne ƙaunar da suke yi wa ƙwallon ƙafa.
Wasan mai farin jini ya kasance wanda ƴan Nijeriya suka fi ƙauna, kuma ya samar da wasu ƴan wasa da suka iya taka leda a faɗin duniya da suka haɗa da JJ Okocha, Nwankwo Kanu, Vincent Enyeama da Victor Osimhen.
Ƴan Nijeriya da dama suna da burin mallakar ƙungiyoyin ƙwallon ƙafa.
A shekarar 2024, an yi ta yaɗa jita-jitar cewa buloniya Aliko Dangote yana da sha'awar sayen kulob ɗin Arsenal na gasar Firimiya ta Ingila amma daga bisani ya fasa cinikin.
Attajirin ɗan Nijeriyar mai harkar mai, a lokuta da dama ya kasance mutumin da ya fi kowa kuɗi a Afrika, a cewar mujallar Forbes.
Renon masu baiwa
Amma ƙaunar harkokin wasanni ya yaɗu har tsakanin fitattun mutane, ɗaya daga cikinsu Tems da ta taɓa lashe kyautar Grammy, wacce a baya bayan nan ta bi sahun ƴan Afrika masu tashen mallaka ko kuma sa hannun jari a ƙungiyoyin ƙwallon ƙafa da dama.
Mawaƙiyar ta waƙar Love Me Jeje da ta yi shura ta shiga cikin tawagar waɗanda suka mallaki ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta San Diego a matsayin mamallakiyar ƙungiyar ta hannun kamfaninta mai suna The Leading Vibe, a cewar wata sanarwa ta bakin kulob ɗin SDFC, ranar Larabar makon da ya gabata.
Ta zamo mace ƴar Afrika ta farko da take da haƙƙin mallaka a gasar ƙwallon ƙafa ta Amurka, wato Major League Soccer (MLS).
Ta bi sahun jerin masu zuba jari gwanin sha'awa, da suka haɗa da wanda ya taɓa lashe gasar Cin Kofin Ƙwallon Ƙafa na Duniya Juan Mata da kuma attajiri a wasannin nishaɗi, Ba'amurke ɗan asalin Senegal, Issa Rae, waɗanda su ma masu hannun jari ne a ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta San Diego.
"Na ji daɗi da na shiga cikin tawagar waɗanda suka mallaki kulob ɗin San Diego da kuma kasancewa wani ɓari na kulob ɗin da ke yaba basira, al'ada da kuma tasirin al'umma," Tems ta bayyana a wata sanarwa da ta aika wa manema labarai.
"Ƙwallon ƙafa tana da wata hanya ta musamman da take iya tattaro mutane waje guda, kuma na ji daɗin taimakawa a gina wani abu na musamman a San Diego, birnin da ya bunƙasa sakamakon bambance bambance da ƙirƙira."
Saka hannun jarin da ta yi na haɗin gwiwa ne da Pave Investment, wani kamfanin zuba jari na Afrika mai zaman kansa da a baya ya jagoranci wata tawagar masu zuba jari a NBA Afrika.
A wani fefen bidiyo da aka wallafa a shafinta na Instagram, mawaƙiyar ta ce: "Na yi amanna waƙa da wasanni sun yi kama da juna ta yadda su biyun suke bai wa matasa masu baiwa dama.
Na so kasancewata cikin wannan aikin musamman ma tare da shirin Right to Dream Academy wajen reno da bunƙasa matasa masu basira. Na yi imanin hakan zai yi kyakkyawan tasiri a kan wasu da dama.
Mawaƙiyar ta tabbatar a hirarrakinta da suka gabata cewa an kyare ta saboda muryarta lokacin tana jami'a.

Mallakar Afirka
An bayyana ra'ayoyi mabanbanta game da labarin mallakar kulob da ta yi.
Lawrence Chuma, wani magoyin baya a Zimbabwe ya sheda wa TRT Afrika: "Wannan ai kyakkyawan yunƙuri ne Tems ta yi! Ina son yadda mawaƙan Nijeriya ke tsarawa da kuma mayar da hankali wajen ganin haƙarsu ta cim ma ruwa."
Wata mai goyon baya a Nijeriya ta ce: " Ko shakka babu, babban mataki ne a wajen Tems. Ina ma a ce da a nahiyar Afirka ta zaɓi wani kulob ɗin. Zama ko da ƙaramin mai hannun jari ne a wata ƙungiya a Afrika da ko shakka babu zai iya taimakawa wajen bunƙasa masu basira."
Ba Tems ba ce fitaccen mutum na farko daga Nijeriya da ya mallaki kulob ɗin ƙwallon ƙafa.
A ƙasa ga jerin ƙungiyoyin ƙwallon ƙafa mallakin fitattun ƴan Nijeriya da suke da sha'awar bunƙasa shauƙin wasan a ƙasar.
Ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta 30BG Sports Club - mallakin mawaƙin Afrobeats Davido an saka sunan ne bisa la'akari da magoya bayansa the 30 billion gang. An ƙaddamar da ita a 2024 a matsayin wani ɓangare na gasar Lagos Liga a watan Nuwamba, yayin da ƙungiyoyi 16 suka fafata domin lashe kyautar Naira miliyan 50 ( bisa ƙiyasi dalar Amurka 33,000). Ƙungiyar da ta lashe gasar, Primal Sporting, ƙwararren masanin fasahar nan na Nijeriya,Mahmud Ribadu ne ya kafa ta.
Ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Tacha FC - Wannan ƙungiyar mallakin ƴar jarida, ƴar kasuwa kuma mai taimakawa jama'a, ƴar shekaru 29 da haihuwa, Anita Natacha Akide da ake yi wa laƙabi da Symply Tacha.
Ta yi suna a Nijeriya sakamakon bayyanarta a shirin talabijin na Naija TV da kuma shirin tashar MTV The Challenge: Spies, Lies and Allies.
Ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Koko FC - ƙungiya ce mallakin Oladapo Daniel Oyebanjo ɗan shekaru 44 da haihuwa, wanda aka fi sani ta fuskar sana'arsa da suna D'Banj. An saka wa ƙungiyar laƙabinsa, wato Koko Master. Mawaƙin na waƙar Oliver Twist da ta yi shura ɗaya ne daga cikin ƙungiyar MoHit da ta rushe kafin daga bisani ya kafa kansa a matsayin mawaƙi mai zaman kansa.
Ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta SupremosFC - Ita ma an ƙaddamar da ita a gasar ƙwallon ƙafa ta Lagos Liga, wannan ƙungiyar ƙwallon ƙafar mallakin attajirin mawaƙi ne, Don Jazzy wanda ya reni haziƙan mawaƙa da yawa da suka bayyana a fagen waƙa na Nijeriya. Ƙarƙashin kamfaninsa Marvin records, ɗan shekaru 42 da haihuwar ya shirya wa Tiwa Savage, Rema, Wande Coal, D'Banj da wasu da dama waƙoƙin da suka yi shura sosai.
Cibiyar Koyar da Ƙwallon ƙafa ta Burna Boy Football Academy - Ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta mawaƙin da ya taɓa lashe kyautar bajintar mawaƙa ta Grammy, Burna Boy na da hadafin horar da ƴan wasansu domin su iya taka leda a kulob kulob da ke ƙasashen waje.
Ƙungiyar ta ɗan shekaru 33 da haihuwa ita ce kaɗai ba ta halarci gasar Lagos Liga ta shekarar 2024 ba. Amma kuma kamar yadda ƙudurinta yake, an kai wasu ƴan wasanta suna buga wa ƙungiyoyin ƙwallon ƙafa a Turai.
Alamun Gasar Cin Kofin Ƙwallon Ƙafa na Duniya
Ƙungiyar ƙwallon ƙafar Ƙasa ta Nijeriya ta halarci Gasannin Cin Kofin Ƙwallon Ƙafa na Duniya sau shida daga cikin takwas na baya bayan nan, inda suka kuskure halartar waɗanda aka shirya a shekarun 2006 da 2022 kawai. Kuma sun kai zagaye na ƴan 16th a karo uku.
Lokacin da Ƙasar ta fi nuna bajinta a Gasar Cin Kofin Ƙwallon Ƙafa na Duniya shi ne a gasannnin da aka gudanar a shekarun 1994,1998 da kuma 2014.
Masharhantar ƙwallon ƙafa a Nijeriya da yawa sun yi imanin cewa gauraya nishɗantarwa da wasanni kamar yadda mashahuran mutane suka yi, zai iya bayar da damar gano ƴan wasan da kuma ƙarfafa samun damarmakin ɗaukar nauyi na ƙasa da ƙasa ga ƴan wasa masu basira na ƙasar nan.