Natasha Joubert ta yi nasara bayan ta yi ta yunkurin lashe kambin kyau. Hoto: shafin Miss Afirka ta Kudu naTwitter

Daga Charles Mgbolu

Natasha Joubert ta kafa tarihi bayan doke Bryoni Natalie Govender a matakin karshe na gasar sarauniyar kyau ta Afirka ta kudu.

Natasha, sanye da wata doguwar riga mai launin ja, da kyar ta iya duba abokiyar karawarta Bryoni, wadda ke kokarin kimtsa kanta a daidai lokacin da ake shirin sanar da wadda ta lashe gasar.

Jama'ar da suka taru a wajen filin na ta kururuwa cikin murna da jiran jin wadda ta lashe gasar.

A karshe dai Bonang Matheba mai masaukin baki na shirin ya sanar da sakamakon gasar, yana mai cewa Natasha ce....!, hawayen farin ciki ya kasa daina zubowa daga fuskarta.

Natasha Joubert ta doke Bryoni Natalie Govender a gasar karshe da ya dauki hankalin al'umma./Hoto: Miss Afirka ta Kudu, shafinYoutube

Abokiyar karawarta wadda ta zo ta biyu, ta rungumeta tare da sumbantarta, sannan ta koma baya don ba da guri a kafa mata kambin na gasar.

Sarauniya mai barin gado, Ndavi Nokeri ce ta yi wannan karramawa ta al'ada inda ta dora kambin gasar da aka yi wa lakabi da 'Mowana' a kan Joubert tare da mika mata wasu furanye a hannunta.

An sake kida da ya ratsa wajen taron a daidai lokacin da Joubert take taku cikin tafiyar kasaita tana waigawa mutanen wurin, tana dariya da kuka duk a lokaci guda.

Gasar Sarauniyar kyau ta Afirka ta Kudu ta 2023 ta samu halartar jama'a sosai a filin wasa na SunBet da ke Time Square a birnin Pretoria.

Kazalika, akwai jerin masu nishadantarwa da suka yi wasa a wajen, ciki har da Siki Jo-An da Jimmy Nevis da Brenda Mtambo da kuma Robot Boii wadanda suka nishadantar da wasan kwaikwayo, da raye-raye masu daukar hanakli.

Sai dai yanayi mafi daukar hanakali fa aka samu a wannan rana na kan macen da ta lashe gasar ta wannan shekara, Natasha Joubert, wadda ta taka rawar gani tare da gwagwarmaya wajen samun wannan nasara.

Natasha za ta wakilci Afirka ta Kudu a gasar Miss Supranational ta kasashen duniya a 2024. Hoto: Shafin Miss Africa ta Kudu Twitter

''Wannan lokacin shi ne mafi girma a rayuwa. Mafarkin da na fara shekaru 11 da suka gabata, ”in ji Natasha a jawabinta yayin karban kambin.

Natasha, daga Tshwane da yankin Gauteng, ta kammala digirinta na farko a fannin Kula da Tallata Haja, kuma ita ce mamallakiyar shagon dinki na Natalia Jefferys, kamfanin da ta kafa tun tana da shekaru 19.

Ta shiga takarar mafi kyau a gasar 'Miss South Africa 2022', daga baya kuma ta wakilci kasar a gasar 'Miss Universe 2020' a Amurka, amma ba ta iya shiga jerin sunayen mata 21 mafiya kyau ba.

Bayan ta shiga jerin 12 ta bayyana cewa "Abu ne mai kama da mafarki a ce ka dawo an ba ka dama a karo na biyu! Na sani wannan shaida ce da ya kamata na bayyana wa duniya da wani sako mai daraja:"

’yan takara uku da suka zo karshe a gasar za su zama jakadun duniya a manyan kamfanoni da dama. Hoto: Miss Afirka ta Kudu Twitter

Tana da magoya baya da dama, saboda an samu murna da sowa bayan an sanar da samun nasararta.

Wani mai goya mata bata a shafinta na Youtube @wandilemthembu, ya rubuta "Natasha ta yi fice yadda ba a zato. Ita ce ta zama mafi yawan halartar gasa a bana. Ta shirya wa wannan lokaci kuma ta kimtsa halartar matakin karshe."

Natasha ta kara da cewa "Ina son na fuskanci wadannan kalubale sabbi, na girma tare da daukaka a matsayina na mace, sannan a lokaci guda na dinga jin dadin rayuwata."

TRT Afrika