An mayar da Almarar Shanu Dubu, da aka bayar a wani littafi na marubucin kagaggun labaran Turkiyya marigayi Yasar Kemal a 1971 zuwa waka, wadda aka rera a wajen Bukin Wakoki Karo na 51 na Istanbul da aka gudanar a eanae 17 ga Yuni.,
An mayar da kalmomin Kemal zuwa gambizar sauti da amo na wasu mawaka da suka hada da Michael Ellison, Ba'amurke, da Ulrich Mertin, wanda dan kasar Jamus ne.
Ayyukan Kemal sun haifar da fannin nuna kwarewa, so da kuma 'yanci", in ji Ellison wanda ya karanta kusan dukkan litattafan marubucin kagaggaun labaran na Turkiyya.
“Salonsa ya sha bambam gaba daya da na sauran.”
Ellison da Mertin, sun rayu a Istanbul tsawon shekaru. Sun tattauna da TRT World game da yadda suke son kade-kade da wakokin gargajiya na Turkiyya, da kuma yadda tafiyarsu ke ci gaba da kasancewa.
Suna da buri iri daya, kuma sun kawo tunanin samar da Kungiyar Mawaka ta Hezarfen, wata kungiyar mawaka da ke istanbul wadda ta kaddamar da sautin zama a fagen wake-waken istanbul mabambanta a 2010 bayan da suka gamu da juna a Istanbul a karon farko.
Tsawon shekaru, kungiyar ta yi burin samar da wakokin da suka danganci al'adu daban-daban tare da hadin kai da makadan gargajiya.
Michael da Ulrich sun so tallata al'adun Turkiyya ga masu sauraro da yawa.
"Ni dan Jamus ne, shi dan Amurka ne, amma muna kaunar Turkiyya." inji Ulrich.
"Za a iya kallon Turkiyya a matsayin wata matattara ta fasahar kida da waka, duba da tarihinta a fannin adabi da wake.”
Yana tunanin kasar dimbin albarkar al'adu da kasar ke da shi, wanda ke habaka fasahar kida da waka na mawaka daga sauran kasashe, abu ne da ya kamata a sanar da 'yan wasu kasashen.
"Tare da ayyukanmu, muna ta kokarin ganin cike wannan gibi."
'Cigaba da Habaka Marar Iyaka'
Kungiyar mawaka ta hezarfen sun kaddamar da wani shirin wakoki da ake kira "Gaba da Gabas da Yamma" a 2015.
Shirin da Hukumar Bincike ta Tarayyar Turai ta dauki nauyi a tsakanin 2015-2020, na da manufar kulla hadin kai tsakanin mawakan maqam, tsarin wake a Gabashin Duniya, da kuma kirkirar kunshin wakoki na al'adu daban-daban.
A karkashin jagorancin Ellison, shirin ya yi ta shigar da kayan kidan gargajiya na Turkiyya zuwa ga tsarin kade-kade na zamani.
Ellison ya yi bayani kan yadda suka bar kofar bayyana ma'anar shirin a bude.
Ya ce "Bai kamata a ce hanya guda ake da ita kawai ba. Idan kana da mawaka da ke aiki ga wakokin al'adu daban-daban, duk sauran abubuwa za su fito daga wannan aiki."
A karkashin kunshin ayyukan wakoki na "Gaba da gabas da Yamma", a Istanbul da Jamus an gudanar da tarukan karawa juna sani, bayar da horo da lakcoci.
Shirin ya bayar da damarmaki ga matasan mawaka d diadaikun mutane masu sha'awar fadada basira da ilimin waken al'adun Turkawa ta hanyar bayar da horo.
Misalai daga al'adun baka na kudancin Anatoliya kamar wakokin deyis da bozlak, tarukan wakoki na addini kamar na Bukin Mawalawi, bayar da horo kan wakokin gargajiya na Turkiyya da kayan kida na gargajiya irin su kemence da kanun da ney; na daga kayayyakin da suka bayar da tallafi ga mahalarta shirin wajen cimma burinsu da dabbaka alaka tsakanin al'adu biyu.
"Ga mawakan, ba batun kida na Gabas ko Yamma ne, abu ne da ya wuce wadannan yankuna. Ellison ya bayyana cewa abu ne da ya shafi samo abubuwa daga al'adu daban-daban."
Kungiyar ta bayyana cewar suna amfani da wakokinsu wajen karin haske da bayyana ayyukan mawakan Turkiyya.
Ulrich ya ce "Wannan abu ne da ya kamata a yi, saboda Turkiyya na da dimbin ayyukan waka da fasaha.
"Kuma a mafi yawancin lokuta mutanen da ke wajen kasar ba su san haka ba."
Almarar Shanu dubu
Yasar Kemal ya yi tasiri kan Ellison wajen hada wakoki a baya. A 2016, "Ellison ya foto da wani littafi na Kemal Yasar mai suna Masunci ya fusata (Deniz Kustu) a wajen wani babban taro.
Amma kuma Almarar Shanu dubu ne mafi shahara kan cigaban da aka samu in ji Ulrich. Michael ya kuma ce "Saboda abu ne na gaskiya tsantsa".
Labarin da aka bayar a "almarar Shanu dubu" ya shafi kabilar Yoruk ta makiyaya wadda ita ce ta karshe a yankin Cukurova da ke kudu maso-gabashin Turkiyya, wajen da cigaban zamani ya daidaita rayuwar mutanen da suka yi dubunnan shekaru a karkara.
Wakokin sun samu taimako da zaburarwa da salon waken bozlak.
Kaifin basirar zube na Kemal, wanda ya hadu da nasarar sanin zamantakewa da yanayin al'umma, ya sanya mawakan fahimtar su waye za su sauraron ayyukansa a cikin wake da kida don fahimtar al'adun Turkiyya. .
Ma'aikatan shirin na da manufar dasa kwadayi da zaburarwa game da al'adun yankin Anatoliya a zukatan masu sauraron su, ko da kuwa sun fito daga iyalai daya ne.
Suna son masu suraro su bar wuraren wake da bukatar neman sani da fahimtar wadannan al'adu.
Ulrich ya kara da cewa "Zan so na ga mutane sun bar wajen tarukanmu suna cewa 'Kai, na san bozlak da dukkan wannan, amma ana gabatar musu da abubuwa ta hanyoyi daban, tare da ma'anoni daban.' Sannan za a iya cewa akwai karin wasu abubuwa,"
Ya yi amanna da cewa ganin abubuwa na al'adu a sigogi daban-daban ba kamar yadda suke a baya ba, zai bude sabbin shafuka ga wadanda za su kalli wasan, tare da danganta shi da al'adunsu.
Ya ce "Ya kamata mutane su yi alfahari da zama masu son sanin abubuwan da al'adun Turkawa suka kunsa. Wannan na daya daga cikin manufofinmu a ayyukan Hezarfen."