Daga Ayse Betul Aytekin
A wata karamar roba da za ka iya ganin abin da ke ciki, za ka ga wani mai fari da yake gyara fata, wannan babban misali ne ga masana'antar biliyoyin daloli.
Turare da ake sanyawa a hammata, wanda ba shi da sinadarin Aluminium ko Parabens ko turarukan da aka samar daga dakin binciken kimiyya, kuma an samar da shi ne don taimaka wa jiki yayin zufa.
A 'yan shekarun nan, turaren hammata wanda aka yi da hannu yana samun karbuwa, inda ya bambanta kansa daga sauran kayan kwalliya da aka saba da su.
Turaren hammatar ba ya kunshe da abubuwan da suke hana zufa wadanda za su kawo cikas kan daidaiton kwayoyin bakteriya masu amfani da marasa amfani da ke hammatar dan adam.
Ba ya hana mutum yin zufa, saboda fahimtar da aka yi cewa zufa wani abu ne da aka gina jiki a kansa don fitar wasu abubuwa marasa amfani ga jiki.
Yayin da manyan kamfanonin da aka saba da su na kayan kwalliya suke amfani da sinadarai, kamfanin Feride Tekin Seymenoglu wanda yake shekara biyu da kafuwa ba ya amfani da kayan da aka saba amfani da su.
Labarin kamfanin ba wai kawai ya dogara ne kan wata jajirtacciyar mace ba, amma wata ce wadda take son kawo sauyi a masana'antar da ba ta da alkibla.
A yau ana amfani da kayayyakin kamfanin Feride a duka lardunan da ke Turkiyya da kuma fiye da kasashe 10.
Ana samar da kayan kwalliyar ne da hannu ta yadda za a tabbatar suna da rahusa kuma ba sa gurbata muhalli, Feride ta tsaya ita kadai wajen samar da kayan kula da fata ba tare da lalata tsarin jiki ba ko kuma kawo cikas ga yadda yake aiki.
Karance-karancen kwastomomi
Kafin kafa kamfaninta na kayan kwalliya mai suna "Atelier Feride" a shekarar 2021, Feride tana amfani da kayan kwalliya yayin da take nazari da bincike-bincike a kansu.
Ita ba ta san cewa karance-karance da bincike da nazarin da take suna kara saita ta ne a kan hanyar zama mai samar da su ba.
"Ashe ni ban sani ba ina dasa wa kaina harsashin sana'ar da zan yi ne a nan gaba," kamar yadda ta shaida wa TRT World. "A yau ina samar da kayayyaki ga kamfanina wadanda na aminta da su kuma hakan ya zama aikina na yau da kullum."
'Yar kasuwar mai shekara 30 tana da digiri a fannin aikin jinya, ta kara samun horo a fannin kiwon lafiya da furanni masu kamshi, wannan wani muhimmin lokaci ne da hankalinta ya koma kan fannin nazari tsirrai don samar kayan kwalliya da turare da kuma magungunan gargajiya.
Fannin Aromatherapy, yana amfani da mayuka masu muhimmanci da aka samu daga tsirrai wajen samar da lafiyar jiki da ta kwakwalwa, wannan ne kashin bayan sana'arta.
Sabanin wadanda ake samarwa a dakin binciken kimiyya, fannin Aromatherapy yana samar da mayuka daga tsirrai da suke gyara fata.
Misali man Lavender da ake samu a turaren hammata na Feride, yana rage damuwa yana samar da kamshi mai dadi da sauransu. Shakar Citrus Oil yana samar da farin ciki da annashuwa. Man 'ya'yan inibi ana amfani da shi wajen yin man gyaran fata, yana tasiri wajen gyaran fata.
"Ina amfani da mayuka na Aromatherapy ba kawai don kamshinsu ba, amma sai saboda yadda suke amfani ga jiki," in ji ta.
Na kirkiri hanyata
A 'yan shekarun nan, ana samun ci gaba da samun karuwar kayan kwalliya marasa illa a wani martani ga manyan kamfanonin kayan kwalliya da aka saba gani. Ko da yake abin takaici ne ganin yadda sabon fannin ya fara fuskantar kalubalen da ya jawo wa kansa.
Feride ta ce tana tallata kayan kwalliyanta a wani bangare na daban daga kayan kwalliya da aka saba da su, ta ce kyau yana tattare da yin abu tsaka-tsaki da kula daidai gwargwado.
"Kayan da muke amfani da su a kullum suna sa mana sinadarai masu cutarwa, kuma sai aka yi rashin sa'a suna jawo mana matsala a jikinmu," in ji ta.
Masana sun yi gargadi kan hadarin da ke tattare da amfani da mayukan fata, ko amfani da kayan kamfanoni daban-daban kuma sai suka jaddada muhimmancin amfani kayayyaki masu gyara fata.
"Na kirkiri hanyata," in ji Feride. "A matsayina na mai samar da kayan kwalliya, ina cewa kula da jiki daidai gwargwado yana da matukar muhimmanci."
Kayan kwalliya daga turaren hammata da jan baki da ja gira da man lebe da sauransu, Feride ita kadai ta samar kayayyakin kwalliya masu burgewa fiye da 40.
Ko da yake kayan kwalliyarta sun kunshi abubuwa masu muhimmanci: man kare mutum daga rana wanda ake shafawa da rana, da man goge jiki wanda ake shafawa da marece da man da ke hana fata bushewa, da kara sinadarin Vitamin C daga lokaci zuwa lokaci da kuma amfani da man hammata.
"Kamar yadda na yi amanna, zabar man fata mara illa yana da alfanu, wanda yake kare jiki, abin da ke kawo lafiyar fata wadda take bukatar kula a 'yan lokuta," in ji ta. "A kan wannan muhimmin abu ne aka gina falsafar kula da fatan jiki."
Haka zalika kwastominta suna bayar da labarin yadda suka ji bayan amfani da kayayyakin wanda yake bin tsarin wannan falsafar, suna cewa: "Na fara amfani da wannan kayan, kuma bayan wani lokaci ina bukatar kadan ne. Ba na bukatar na rika amfani da shi a kai a kai kamar yadda na yi daga farko."
A bara kadai, an samu kari na adadin kayan da kamfanin Feride yake samarwa da nunki biyar. Kamfanin Feride ya danganta hakan ga gamsuwar da kwastomominsa suka samu, kuma ya ce, "Yayin da ba za mu iya ware wasu kudi don tallace-tallace ba, kwastomominmu suna tallata kayanmu a kodayaushe a madadinmu."
"A matakin samar da kayayyakin, muna sake amfani wasu tsofaffin kayayyakin bakin gwargwado. Hatta lokacin da ake kawo kayan, na yanke shawarar ba zan yi amfani da kayayyaki da za su zama sharar da ba a bukata ba," in ji Feride.
Magana kan kayan ado da kwalliya
Yayin da ake ci gaba da samun isla mai gurbata muhalli na karuwa, hakan wuce batun cutar da muhalli ya kai matakin cutar da mu kanmu. Wannan shigar da wannan tsari a kamfanin Feride yayin samar da kayayyakin.
Duk da cewa akwai rufa-rufa a masana'antar ado da kwalliya kan ainihin abubuwan da ake amfani da su wajen samar da kayyakin, Feride ta lashi takobin cewa za ta tsayuwar daka wajen baje komai a faifai da kuma dorewar abubuwa.
Ta mayar da hankali wajen samar da kayayyaki marasa ila ga muhalli, kayayyakin wadanda ba sa cutarwa ga fata sun bude wani sabon babi kan inganci a masana'antar da ake rufa-rufa.
"Idan ba zan iya samu abu inganci wanda daga shi ne zan samar da kaya, to na gwammace na hakura," in ji ta.
A 'yan shekarun nan masana'antar kayan kwalliya ta yi fama da kalubale da kaya da abin da suka kunsa wanda hakan ya sa an samu rashin yarda daga kwastomomi.
Bincike ya nuna cewa kaso 79 cikin 100 na mutane wadanda suka sayi kayan kwalliya sun nuna shakku dangane da ikirarin masana'antar kan dorewa.
Feride za ta yi tsayuwar daka wajen kare ingancin kayan kamfaninta "magana daya" kamar yadda ta ce, yada bayanan abin da suka kunsa da amfaninsu da alfanunsu da matsalolin kowane kayanta, ta ce za a baje wa kwastomominta komai a faifai.
Kasuwanci a tsanake
Bayan harkokin kasuwancinta, Feride ta dukufa wajen taimaka wa al'umma saboda sauke nauyin da ya rataya a wuyanta na taimaka wa mutane.
Biyo bayan girgizar kasar ranar 6 ga watan Fabrairu, ta fara wani shiri don samar da man shafawa mai warkar da kuraje ga wadanda girgizar kasa ta rutsa da su, wanda yana cikin abubuwan da aka fi bukata, saboda akwai matsalar tsafta a yankin, saboda ba a yi sauya wa yara kunzugun famfas a kan lokaci ko kuma a wanke su yadda ya kamata ba.
Shirin da Feride ta kirkiro yana da aniyyar samar da man kuraje ga wadanda girgizar kasar ta shafa. Ta ce saboda sanyi da matsalar iska, yara da manya jikinsu kan bushe ko tsage ko kuma ya fara zubar da jini.
Tare da taimakon kawayenta ta samar da man kuraje fiye guda duba biyar da kuma adadin man fata mai yawa da sabulai da man da ke kare fata daga hasken rana. Kayanta sun kai kowane birnin da girgizar kasar ta shafa.
Godiya ga kawayenta 'yan sa-kai wadanda suka taimaka wajen aikin, Feride ta shirya samar da kayayyaki cikin sauri wadanda saboda yawansu da sai sun dauke ta watanni kafin ta gama.
Labarin Feride yana nuna jajircewarta a matsayinta na 'ya mace, kuma manuniya ce kan yadda masana'antar ado da kwalliya take boye gaskiya dangane da tasirinta ga muhalli.
Yayin da masana'antar take fama da kalubale masu tarin yawa kamar dorewa da amfani da abubuwa marasa illa da gwaji a kan dabbobi da karkatar da gaskiya yayin tallan kayan da kayan jabu da amfani da robobi masu gurbata muhalli da sauransu, Feride ta yi amannar cewa za a cimma nasara wajen samar kayan ado da kwalliya marasa cutar da muhalli da ma dan adam.