Nuna bambanci tsakanin jinsi a kafofin intanet na ƙara yawa duk da irin kokarin da gwamnatoci a fadin duniya ke yi.  Hoto: AFP

Tsauraran ka'idojin jinsi da son zuciya da kuma hasashe kan yi tasiri sosai ga yanayin mu'amala da kuma damarmaki da yawancin 'yan mata da mata suke samu wajen amfani da kafar intanet, a cewar wani sabon bincike da aka gudanar.

Binciken da aka gudanar kan mata 10,000 'yan shekaru tsakanin 14 zuwa 21 da ke amfani da kafar intanet da iyayensu a kasar Habasha da Kenya da Nijeriya da Tanzaniya da kuma Indiya ya gano cewa ana yawan sanya ido kan mata, kuma tasirin hakan ya kan raunata mata da kuma ''kashe musu gwiwa wajen a dama da su a kafar ta intanet.''

''Sakamakon hakan kan sanya 'yan mata daukar matakin kare kansu wajen rage yanayin huldarsu da mu'amalarsu har da musayar bayanan sirri ta kafofin yanar gizo,'' a cewar rahoton bincike da kungiyar Girl Effect ta Malala Fund wacce ke karkashin Asusun kula da kananan yara ta MDD, UNICEF da kuma gidauniyar Vodafone Americas suka fitar.

"Tasirin hakan ba wai kawai yana tsayawa ga yanayin samun damar amfani da kafar intanet da 'ya'ya mata kan yi ba ne, amma yadda wadannan halayya kan kashe musu ƙwarin gwiwa da kuma tsara yanayin tunaninsu wajen amfani da kafofin intanet don samun damar biyan bukatunsu na zamantakewa da samun ilimi da bayanai masu amfani," in ji rahoton.

Rage karsashi

Nuna bambanci tsakanin jinsi a kafofin intanet na ƙara yawa duk da irin kokarin da gwamnatoci a fadin duniya ke yi.

Wani bincike da UNICEF ya gudanar a farkon wannan shekarar ya nuna cewa a kasashe 54, cikin matasa maza da mata 100 da ke amfani da intanet kashi 71 na 'yan mata suke amfani da kafar.

A lokaci guda, mata sun fi fuskantar cin zarafi ta yanar gizo, kuma cin zarafi yana sa 'yan mata barin shafukan sada zumunta irin su Facebook da Instagram, kamar yadda binciken da aka gudanar na kwanan nan ya nuna.

Daga cikin matasan maza da mata da ke da mu'amala da kafofin sada zumunta na zamani, kashi 12 cikin100 na yara mata sun ce suna taka tsan-tsan yayin da suke amfani da kafofin na intanet.

Sannan kashi 11 cikin 100 kuma ba sa kaunar yada hotunansu da sharhi ko mayar da matarni kan wani abu da aka wallafa fiye da maza da ke tsakanin shekarunsu, a cewar rahoton.

Yayin da son zuciya da tsoron cin zarafi suke takaita mu'amalar 'yan mata a intanet, yawanci mata ba su cika kallon kansu a matsayin masu fasaha ba balle su iya tunanin akwai wata dama da intanet zai iya samar musu wajen ci gaban rayuwarsu, a cewar rahoton na kungiyar Girl Effect.

Ilimin fasahar intanet

“Illar hakan ya haifar da koma baya ga ‘ya’ya mata, la'akari da yadda suke guje wa ilimin fasahar intanet sakamakon tunaninsu na cewa babin ba nasu ba ce, kuma ya sa ake kallon tabbas fasahar ba tasu ba ce saboda guje mata da suke yi, in ji rahoton.

A matsayin matasa da ke takaita bincike da rage mu'amalarsu da kafar yanar gizo,'' a lokuta da dama mata sukan dauki wannan dabi'a da halayya zuwa wuraren aikinsu, inda suke fuskantar matsaloli wajen nuna ƙwarewarsu da basirar inganta ayyukansu," a cewar Mitali Nikore, ƙwararriya wajen tsara manufofin jinsi a ƙungiyar bincike ta Nikore Associates.

"Tasirin hakan, yana haifar da mummunar illa ga yanayin mu'amalar mata a wuraren aiki, kuma yana rage damarsu ta samun aiki da kuma ƙwarewa a fannoni da dama har da hanyoyin samun kuɗaɗen shigarsu," in ji kungiyar Nikore.

Baya ga manyan wayar salula na zamani da yara mata da 'yan mata suke samu, akwai bukatar a samar musu shirye-shiryen ilimin fasahar intanet, sannan a yi ƙoƙarin daƙile duk wasu ƙa'idoji na nuna wariyar jinsi a intanet, in ji Nikore.

Rashin sanya dokoki

''Dole ana damawa da 'yan mata wajen samar da ƙirƙiro da fasahohi da za su amfani bukatunsu,'' a cewar mai magana da yawun kungiyar Girl Efeect.

Alal misali, kungiyar Gilr Effect ta kirkiro da wata manhaja ta mutum-mutumi a Afirka ta Kudu da Indiya - da ke iya tattaunawa da 'yan mata kai tsaye mai suna ''Big Sis and Bol Behen'' (ki gaya mini, 'yar'uwa) - don taimaka musu wajen samun sahihan bayanai kan batutuwan da suka shafi lafiya gabakidaya ciki har da lafiyar jima'i ga 'yan mata.

Duk da cewa sabbin dokokin da aka samar kamar ''Dokar Tsaron Intanet ta Biritaniya da kuma Dokar Tsaro Kan intanet ga Yara a Amurka za su iya taimaka wa wajen kare yara, ''wadannan ƙa'idojin za su iya aiki ne na dan wani lokaci, kuma galibi suna baya a ci gaban fasahar zamani da ake samu," in ji mai magana da yawun kungiyar ta Girl Effect.

''Yara mata da 'yan mata matasa suna bukatar a dama da su wajen ƙirƙirar fasahohi da za su samar da mafita; domin suna da hikima da basira da za a iya amfani da su a intanet don samar da sauki da aminci a kafar ta yanar gizo."

TRT Afrika