Daga Hamisi Iddi Hamisi
A tsibirin Unguja da ke kusa da gabar tekun Tanzania, ’yan mata ne suke tarbar baki dauke da kayan aikinsu na zanen lalle.
Zanen lalle mai dadadden tarihi da suka gada tun aru-aru ya zama hanyar cin abinci a gare su bayan talauci ya hana su samun damar cigaba da karatu.
Zanen flawa da suke yi na lalle yana cikin abubuwan da suke kayatar da baki masu zuwa shakatawa a gabar tekun na Indiya.
A yankin Mji Mkongwe, ’yan mata kamar Zuwena Abdallah sun bayyana yadda suka kware a zanen lallen tun suna sakandire a wani yanayi kamar na sana’ar da suka gada tun iyaye da kakanni.
Bayan kammala makaranta, da kuma rashin damar cigaba da karatu, sai ta koma yin lallen, wanda Larabawa ’yan kasuwa suka zo musu da shi yankinsu tun a shekarun baya.
“Bayan kammala sakandire ne na yanke shawarar fara sana’ar lallen domin samun kudin da zan cigaba da karatu a kwaleji,” kamar yadda Zuwena ta shaida wa TRT Afrika.
Ta ce sana’ar tana ta’allaqa ce da zuwan baki masu shakatawa tsibirin, inda ta kara da cewa tana samun kusan Dala 120 a duk wata.
“Da na kammala karatun sakandire, sai na fara sana’ar lalle saboda rashin kudin da zan shiga kwaleji,” inji Zuwena.
Tana cikin matan da ake dauka domin yi wa amare lalle da sauran zane-zanen ado.
Sana’ar lalle
Kasar Tanzaniya ta dade tana fama da matsalar rashin aikin yi, wanda hakan ya sa matasa da dama suka koma sana’ar lalle a matsayin hanyar samun abin sakawa a bakin salati.
Ana koyon sana’ar ce a wajen waxanda suka kware, amma akwai makarantun da aka assasa na musamman domin koyar da sana’ar tare da inganta ta.
Hassan Kimbwembwe, daraktan cibiyar koyar da sana’a ta Helping Hand for Relief and Development Tanzania (HHRD), ya ce matasan suna amfani da sana’ar ta lalle domin samun jarin fara wata sana’ar ko wata kasuwancin daban.
“Babbar manufar ita ce horar da su sana’o’i da domin suma su koyar da wasu matasan saboda su dogara da kansu,” inji Biban Dewji mai koyar da lalle a cibiyar.
Dalibai masu hazaka za su iya kwarewa a lalle a tsakanin wata biyu, amma wasu sun yi kusan shekara daya suna koya.
Illarsa ga lafiya?
Babu wata illa da aka tabbatar lalle na jawowa ga lafiya kamar yadda masu bayar da horon, da masana kiwon lafiya da masu amfani da lallen suka bayyana.
Sun bayyana cewa hada garin lalle da lemu da ruwa yana taimakawa wajen kara tsayin gashi, duk da cewa ba a tabbatar da hakan ba a kimiyance.
Zanen lalle na kama da zanen tatu, amma lallen na saurin gogewa.
Zanen lalle ya kasance daya daga cikin kwalliyar mata a yankin Gabashin Afrika na daruruwan shekaru. An fi rububin lallen ne a lokutan bukukuwa na aure da idi biyu a yankunan da Musulmi suka fi yawa.
Amma fasahar na kara samun karbuwa, sannan ana kara samun wasu sababbin ci gaba a zane-zanen wadanda suke yin daidai da zamani.