Daga Fathiya Bayusuf
Furanni da tashin kamshinsu wani muhimmin bangare ne a al'adun Swahili a yankin gabar tekun Gabashin Afirka wanda ya taso daga kudancin Somaliya zuwa arewacin Mozambique.
Alamomin soyayya da suke nunawa ya samo asali ne tun karnoni da suka gabata lokacin da 'yan kasuwa Larabawa da Iraniyawa suka ratsa ta tekun Indiya bayan yanayin damuna.
Ado da soyayya ba sa cika a tsakanin 'yan Swahili da ke yankin Gabashin Afirka ba tare da furanni ba - ana amfani da su wajen turara gidajen amare sannan mata na sanya su a matsayin kayan kwalliya.
Furanni sun zama tamkar wani abin amfani na dole ga amarya da ango a lokutan bukukuwansu na aure.
Curin furen Swahili ya kunshi nau'in fure na wardi da jasmine da kuma kiluwa - wani nau'i na furannin Magnolia, launi da haskensu da kuma irin kamshinsu da ke tashi mai dadi ya sa suka yi fice.
Ana iya hada furen su zama kayan kwalliya na tattara gashin mata da ake kira da vikuba ko shada a harshen Swahili ko da yake sun danganta da yanayin girmansu sannan ga maza ana hada furanni da ake ratayawa a wuya da aka fi sani da koja.
"Sun ce kyawun mace 'yar Swahili ya ta'allaka ne ga tsabta da kuma kamshinta a ko da yaushe, musamman idan ta tsara wankanta da furanni masu kamshi," kamar yadda Fatma Mohammed, wata mai sana'ar curin furen Swahili a birnin Mombasa mai tarihi ta shaida wa TRT Afrika.
"Wadannan furanni suna da matukar daraja a cikin al'umma, a duk lokacin da mace ta sanya vikula, kyawu da kuma kimarta na dada karuwa, "in ji ta.
Ana hada kayan kwalliya na mata da maza ta hanyar jera furanni da zare da allura.
Kazalika, ana sanya curin furen a cikin gida don turara wuri da kuma kawar da wari; ana iya sanya su a cikin falo ko dakin kwana.
“Mace za ta iya sanya kishada a gida, yayin da take dafa wa mijinta abinci da ‘ya’yanta, haka kuma yana kara sha’awa da soyayya tsakanin mata da miji,” in ji Fatma Mohammed.
Hada ire-iren wadannan kayayyakin ado na gargajiya ya samar da guraben aikin yi ga mata da dama a Mombasa.
Masu aikin hada furannin sun himmatu wajen koya wa 'yan baya wannan sana'a don tanada al'adar kayayyaki na ado mara gushewa.
"Ina taya Mama Fatma hada koja - tana rike karshen bangaren zaren yayin da nima nake rike da dayan sai mu yi ta aikin saka furen jasmine a jiki, ina taimaka mata ne saboda wani lokacin idan ba ta kusa, sai na hada makoja ko vikuba da kaina, na sami kwarewa sosai daga wurinta." kuma ina godiya saboda ina samun kudin shiga," in ji Tima Moh'd, wata mace hazika mai tasowa.
Furen Swahili ya kara fice tare da samun ci gaba a Mombasa sakamakon yanayin bukatunsa a taron bukukuwa daban-daban.