A lokacin kuruciyarta, akan kira Yinka da mai katon ciki/ Hoto: Yinka  

Daga Pauline Odhiambo

Da farko dai, aikin Yinka Olowokere na kirkiro abubuwa masu ban sha'awa da daukar hankali ya sa ta yi fice musamman idan aka yi la'akari da kayyadaddun ka’idojin shafin Instagram, inda take baje-kolin ayyukanta na kirkire-kirkire.

Duba da irin kuzari da karsashi da matashiyar take nunawa, ana iya cewa hakan na da alaka da bakin ciki da kuma tabon da ta yi fama da su kan cin zarafin halittarta, yanayin da ya zaburar da ita wajen yaki a kansu.

"A lokacin da nake tasowa, mutane sun fi sani na da yarinya mai katon ciki," a cewar Yinka wacce ta kafa kungiyar "No to Body Shaming" a hirarta da TRT Afrika inda ta bayyana irin kuncin da ta shiga a lokacin yarintarta a jihar Ondo ta Nijeriya.

“A lokuta da dama, nakan ci abinci sau daya a rana kawai saboda rashin wadata, kuma irin abincin da nake ci shi zai taimaka min a tsawon yinin, ko a cikin kayan makaranta, cikina yakan bayyana kasancewar a koyaushe ina fama da matsalar girman ciki."

Wannan yanayi na sanin kimar jikin dan'adam tun daga lokacin kuruciyar Yinka ya dasa mata rashin tsoro a rayuwarta, ta taso da shi a zuciyarta har zuwa lokacin da ta fara tallan kayan kawa a shekarar 2014 lokacin da take karatu a fannin kade-kade da waka a Kwalejin Kimiyya da Fasaha ta Ibadan.

Duk da yawan aibantata da mutane ke yi, Yinka ba ta yi kasa a gwiwa  ba wajen yin Modelling ba/ Hoto: Yinka

Nauyin da ke kan sarauniyar kyau

A makaranta, Yinka ta fara gasar farko ta sarauniyar kyau inda matashiyar 'yar shekara 26 a yanzu ta lashe taken "Sarauniyar Hall" matsayin da ya sauya mata rayuwarta, inda ta yi ta samun ci gaba.

A lokacin, Yinka na sanya kaya lamba takwas, ma'auni mafi karanci ga mutum siriri.

"Lokacin da na fara samun horo sosai kan tallan kayan ƙawa, na lura cewa an fi mayar da hankali kan siraran mata," in ji ta.

"That realisation made me start shaming my body because I felt like I was doing something wrong." Yinka always felt like the "bigger" girl on set, with many of the other models ranging from sizes zero to 4. "I even joined a dance crew because I thought it would be a fun way to lose weight," she tells TRT Afrika.

"Sanin hakan ya sa na fara aibata surar jikina, don ji nake yi tamkar na aikata wani laifi." Yinka ta kan ji kamar ita kadai ce mai babban jiki a tsakanin abokan gasarta, inda yawanci masu jiki lambar sifili ne zuwa hudu.

''Na shiga cikin kungiyar rawa saboda a ganin hakan zai taimaka min wajen rage ƙibar jikina,'' ta shaida wa TRT Afirka.

Sai dai wannan nauyin na batun rage ƙiba da ke zuciyar Yinka ya daɗa girma yayin da ta kai matsayin ƙwararriya a fannin sana’ar tallan kayan ƙawa, inda ta yi waiwaye kan yadda takwarorinta da masu daukar hoto da kwaliyar fuska da na kayan sawa suke aibata siffar halittarta.

A tsawon lokacin da Yinka ta kwashe a sana'ar Modelling ana yawan aibanta halittarta / Hoto: Yinka 

Ta tuna yadda wata mai kwalliyar fuska ta ci zarafin halittar gashin idonta sakamakon kasancewar "ƙanana ne sosai''. Mai gyaran ta yi min abun da ya baƙanta min rai a wajen taron gasar kyau da aka yi.

"Sai kawai na ji ta kama kunkumina ina zaune ta ce, 'Idan za ki iya cire wannan, za ki fi yin kyau'," in ji Yinka.

"Na ruɗe saboda ba a zaune nake ba balle na yi tunanin ko kitsen jikin kuguna ne ya fito. To me yasa za ta yanke min hukunci a kan yanayin halittata?"

Ire-iren wadannan kalamai sun yi tasiri sosai a zuciyar Yinka, lamarin da ya taɓa ƙimar darajarta.

Cika giɓin

Duk da sukar da ake yi mata, Yinka ta dage wajen sana'arta ta tallan kayan ƙawa, a hankali a hankali ta fito da wata baiwa da ta zarce halittar jikinta.

"Na fahimci cewa mutanen da ke aibata yanayin halittar ɗan'adam suna fama da rashin tsaro ne su kansu.

Wannan fahimtar ce ta kawar min da tunanin cewa masana'antun kyau na samun cikakkiyar halittar jiki, daga nan na fara zama mai son kaina da kuma godiya ga irin halittar yadda jikina yake," in ji ta.

Ci gaban da Yinka ta samu wajen ganin ƙimar kanta bai wuce hakan kawai ba.

A shekarar 2020, ta zo ta biyu a gasar kyau da aka yi sannan an zabe ta don wakiltar kasarta a Afirka ta Kudu.

Sai dai murnar Yinka ya koma cikin bayan da masu shirya gasar daga Afirka ta Kudu suka tuntubi kamfanin da take aiki kan cewa ba ta cika ka'idojin da suke nema ba.

Yawan aibata halittar Yinka a masana'antar kyau ya yi tasiri wajen taɓa darajar ƙimarta./ Hoto: Yinka 

"An shaida min cewa kamfanin ya ki amincewa da ni ne saboda ba a sanar da su cewa 'yar takarar sarauniyar kyau daga Nijeriya ta zama mai 'ƙiba' ba," in ji Yinka, wacce a lokacin girman jikinta ya kai lamba goma.

"Na zo karshen duk wata gasar sarauniyar kyau, domin ba zan iya ci gaba da ƙuntatawa kaina a kan ra'ayin mutane ba game da yadda halittar jikina ya kamata ta kasance ba.

"A yanzu haka ina cikin shauƙi kan yadda nake, sannan ba na bukatar samun tabbacin wani kan hakan," in ji ta.

Abar koyi

Abin da ya faru da Yinka ya jefa ta cikin shakku na cin zarafin halittar jikin ɗan'adam da ake yawan yi, yayin da ta soma mayar da hankali ga sabon aikinta na tsayawa a bayan kyamara a matsayin mai daukar hoto da bidiyo ta wayar zamani.

Sannan ƙwararriya ce a kafafen sada zumunta. Matashiyar ta zaɓa wa kanta yin bincike kan yadda masana'antar waƙoƙi ke ba da goyon baya ga wannan batu na cin zarafin halittar mutum.

"Wannan ne ya sa na fara ganganmin 'No to Body Shaming' a shekarar 2020. Ina so in ƙarfafa gwiwar yabo da son yanayin halittar jikin mutum da kuma samun kwanciyar hankali da yanayin fatar jikin mutum a duk yadda take," in ji ta.

Gangamin Yinka na yaki da cin zarafin halittar jikin mutum ya taimaka wa mata dawo musu da kimarsu. Hoto: Yinka

Tun da ta kafa wannan kungiyar, Yinka ta mai da hankali wajen fitar da take yi a kowace shekara da za a dinga duba tare da ƙarfafa gwiwar mutane kan yanayin halittarsu daban-daban.

Taken taron na bana ya ta'allaka ne kan ƙara ƙwarin gwiwa ga yara 'yan kasa da shekara 14.

“Yawancin yaran da muke aiki da su iyayensu ko ‘yan’uwansu sun aibata yanayin launin fatar jikinsu, har ma da yanayin girman kai ko girman jikinsu, wanda hakan bai dace ba,” in ji Yinka.

Yinka ta kaddamar da wani littafi da zai taimaka wa yara 'yan kasa da shekara 14 son yanayin jikinsu./ Hoto: Yinka

"Muna taimaka wa yara, su fahimci cewa jikinsu na kan gaba tare da kyautata wa kansu da sauran mutane, saboda tasirin cin zarafi ko aibata yanayin halittar jikin mutum kan haifar da matsala ta lafiyar ƙwaƙwalwa."

A matsayin wacce ta taɓa fadawa cikin yanayi na tsanar kanta, a yanzu Yinka ta mayar da hankali wajen ilimantar da mutane lokaci da kuma yanayin da ya kamata su furta "a'a" a rayuwarsu.

TRT Afrika