Har yanzu babu isassun emoji da ke wakiltar alwadun Afirka. Hoto AA

Daga Dayo Yussuf

A lokacin da fasahar sadarwar yanar gizo ke kara bunkasa, mutane a sassan duniya na ci gaba da amfani da alamun sako, hotuna da surori don sadarwa da isar da sako ko halin da suke ciki a shafukan sada zumunta.

Wasu masu amfani da irin wadannan alamomi a shafuka daban-daban na cewa suna taimaka musu wajen bayyana tunani ko wani ra’ayi da suke da shi. Wasu ma na cewa ba sa iya aika sakonni ba tare da alamomin emoji ba.

“Alamomin emoji sun zama wasu ginshikai a tattaunawa ta yanar gizo. A lokacin da ka aika da rubutaccen sako, ba ka ganin mutumin da kake magana da shi, so ba za ka san ta yaya yake fahimtar ka ba,” in ji Sharon Machira, mai yawan amfani da alamomi da ta tattauna da TRT Afirka a Nairobi babban birnin Kenya.

Sharon ta bayyana cewa rubuta sakonni ba tare da alamomi, kamar magana ce ba tare da motsa jiki ba. Saboda muhimmancin wadannan alamomi ne aka sanya ranar 17 ga Yuli ta zama Ranar Alamomin Emoji ta Duniya.

Dabarun iya rubutu

Alamomin emoji sun bambanta da juna, kuma yanayin su ne ke bayyana a ina za a yi amfani da su, ko kuma al’adun mutane ne ke ba su ma’ana.

Sharon ta kara da cewa “Za a iya rasa abubuwa da dama idan ba a yi amfani da alamomin emoji ba a yayin aika sako. Amma idan ka yi amfani da su… zan iya cewa yauwaaaa ya fahimci me na ke cewa.”

Amma kuma yadda ake yabon alamomin emoji, a daya bangaren kuma za su kuma cutar da al’umma. Masanin zamantakewar dan adam Dr. Kennedy Ong’aro ya ce alamomin emoji sun yi tasiri kan iya yare sosai a tsakanin mutanen yau.

Dr. Ong'aro ya ce “Mutane sun sabarwa da kawunansu al’adar amfani da gajeriyar hanya a yayin aikata kowanne abu.”

Fadaduwa

“Harshe jigo ne na sadarwa. A lokacin da ka yi amfani da alamar emoji, ka kaurace wa rubuta kalmomi kenan.

Hakan na sanya mutum asarar kwarewa wajen rubutu, kun ga kenan za mu kare da samun al’ummar da ta dogara kan hotuna da surori don bayyana kanta, maimakon amfani da kwararren yare.” Dr. On’garo ya shaida wa TRT Afrika.

Sadarwa ta yanar gizo al’amari ne da gama-gari da ya game kowanne bangare. Matashi da ke aika sako ta wayar hannu a yankin Arusha na Tanzania, daya yake da matashin da ke yin hakan a Tokyo da ke Japan ko Alkahira da ke Masar.

A saboda haka, hanyar aika sakonni da fasahar da ake amfani da ita wajen aika sakonnin duk daya ne.

Amma bayan amfani da alamomin emoji ya samu shuhura, sai aka fara yin korafi cewa wadannan alamomi ba sa wakiltar al’adu da dama, musamman na Afirka, wanda wannan abun dubawa ne.”

“Kaiii! Kayyasa!” Da jin haka ko ganin an rubuta za kasa mai fadi ko rubun ya yi mamakin wani abu, ko ka ji an ce ko rubuta “Heheheheeee, mmmmmmmmh,” kalamai ne na muzantawa.

"Amma idan a Afirka ka ke b aka bukatar a fada maka ma’anar “Mscheeeew”. Da ka ji ka san ka yi wa wani laifi ne.

Amma za ka iya bayyana wadannan kalmomi a sakon da kake tura wa wani ta hanyar amfani da alamomin emoji, shi ya sa ‘yan Afirka ke son a samar da emoji da suke da ma’anar al’adun Afirka.

A 2018, mawakin kasar Ivory Coast, O”Plerou Grebet ya kaddamar da wasu alamun emoji na Afirka. Ya ce “manufata ita ce na samar da alamomin emoji da ‘yan Afirka za su yi amfani da su”.

Grebet ya kara da cewa manufarsa ita ce daukaka Al’adun Afirka a duniya.

Alamomin Emoji na Afirka

‘Afirka na da kyawawan al’adu masu ban sha’awa da suke da ado da dama, wadanda ba a nuna wa duniya su ta hanyar alamun emoji. Mutane na tunani Afirka kawai matsala ce, wanda ba haka ba ne.” inji Grebet.

Idan ka kalli manhajar da Grebet ya samar mai suna ‘’Zouzoukwa’ akwai alamun emoji sama da 390 da ya kirkira da kansa, sun hada da yadda ake bayyana mamaki a Afirka, dariyar Afirka, abinci da tufafin Afirka.

Amma idan ka yi magana da kwararru kan zamantakewa, musamman na zamani na daban, za ka ji wasu na bayyana ra’ayinsu game da wadannan alamomi.

Dr Ong’aro wanda shi ne shugaban tsangayar nazariyyar zamantakewa a jami’ar Daystar da ke Nairobi, ya ce akwai hatsarin rashin fahimtar emoji, saboda yadda suke takaita bajinta da kaifin basirar matasa yayin sadarwa.

“Misali, idan za ka bayyana farin ciki akwai alamar emoji ta ‘Smiley’, amma wannan wani mutum daya ne ya samar da ita. Hatsarin shi ne kowa ya ta’allaka da wannan wajen bayyana farin cikin sa ba tare da tunanin wata hanyar ta daban ba. Hakan na kawo lalaci ga matasa.”

Kebantuwa daga jama’a

Amma muhimmancin emoji ya bambanta daga zamani zuwa wani. “Emoji sun kirkiri sabon yare da al’adunsu na yanar gizo,“ in ji Sharon, wanda ke wakiltar matasa ‘yan kasa da shekaru 30.

“Misali, emoji din makara na nuni ga mutuwa. Amma a lokacin da muke musayar sakonni da abokaina sai muka rubuta alamar makara, hakan na nufin kana kashe ni da ban dariyarka,” in ji ta.

Emoji din babban dan yatsan hannu na nufin ‘EH’ ko ‘OK’. Amma nan da shekaru biyar ko goma ba mu san ma’anar da wannan emoji na babban dan yatsa za ta zama ba. Wannan ne ya sanya alamomin emoji ke da dadi wajen sadarwa.”

A nasa bangaren, Dr. Ong’aro ya dage kan cewa emoji na kebantar da wasu mutane a yayin sadarwa. “Saboda ana mafani da emoji da yawa, suna da ma’anoni daban-daban da suk dogara g al’ada. A saboda haka, sakon na iya gurbata, musamman ma a tsakanin matsa da tsofaffi.”

A yanzu akwai alamun emoji sama da 4,000 da ake amfani da su a addinai, al’adu, yankuna da tsakanin masu shekaru daban-daban a duniya. Tare da yadda ake samun sabbin emoji a koyaushe, akwai yiyuwar a ci gaba da ganin sabbi kar na ta bullowa.

TRT Afrika