Kauyen Siby, mai nisan kilomita 50 daga Bamako babban birnin Mali, ya yi fice wajen fentin gidaje masu kyau.
Yawan yi wa gida fenti wata al’ada ce a kauyen. Amma Soumaila Camara mai shekara 42, ya kara wa wannan al’ada karfi.
A 2014, ya kirkiro wani biki na shekara-shekara domin a raya al’adar da kuma jawo hankalin masu yawon bude ido. Tun daga lokacin wannan ala’da ta yi ta habaka.
“Bayan girbe amfanin gona, iyayenmu sukan yi wa gidajenmu da kauyenmu ado da fenti domin maraba da sabbin haihuwa da kuma murnar bukukuwa wadanda ake yawan yi a lokacin zafi kafin saukar ruwan sama,” kamar yadda Soumaila Camara ya shaida wa TRT Afrika.
Kauyen Siby yana da mazauna kusan 28,000. Mata na taka muhimmiyar rawa wurin gini da kuma kayata gidajen.
“Kwalliyar gidaje aikin mata ne. Su ne suke yin kwalliyar, da zanen da sauran hada launuka,” in ji Mista Camara.
Matan suna amfani da buroshi inda suke yin fentin a launuka daban-daban a duk shekara.
Akasari gidajen laka ne. Baya ga bukukuwan suna da na aure, Soumaila Camara ya ce ana bikin kaciya ga yara maza a kauyen bayan an kammala gyaran gidajen.
“Tun 2014, akwai masu yawon bude ido da dama da suka soma sha’awar kauyenmu. Muna aikin samar da wata cibiyar wayar da kai da ake kira Siby Tourism domin nuna abubuwa masu kyau game da kauyenmu,” in ji Mista Soumaila.
Haka kuma domin kara karfin gwiwa ga mazauna kauyen Siby domin su ci gaba da wannan al’ada, ana bayar da kyaututtukan kayan sawa da fatanya da sauran kayayyaki ga matan da suka fi kwazo wurin yi wa gida kwaliyya.
“Bikin namu yana fito da yadda matan Afirka suke da kuma nuna muhimmiyar rawar da suke takawa a cikin iyali a Afirka,” kamar yadda Camara ya kara da cewa.