A kasa mai dumbin al'adu, bikin na nuna muhimman al'adunta ta hanyar raye-raye da wake-wake da zayyana da adabi tare da bai wa mutane damar bayyana fasaharsu. . Photo: TRT Afrika

Daga Kudra Maliro

A kan debi kwana 10 tun daga ranar 6 ga watan Yuli ana gudanar da wani bikin al'ada a garin Mopti da ke yankin tsakiyar Mali. Abubuwan da ake gudanarwa a wajen bikin kamar fareti da gabatar da wakokin baka da na gargajiya da raye-raye na farfado da nishadin kasar wacce ke cikin rikicin siyasa.

Bikin al'ada mai suna Biennale artistique et culturelle du Mali da Faransanci, wani babban biki ne da ake nuna al'adun Mali da nuna irin yawan kabilunta.

A shekarar 2010 sai da aka dakatar da gudanar da bikin, wanda aka fara shi tun a shekarun 1970, sakamakon hare-haren masu ikirarin Jihadi da suka addabi arewacin Mali.

Oumar Koita, wani matashin shugaban al'umma daga Mopti, ya shaida wa TRT Afrika cewa bikin al'adar na da muhimmanci ba kawai don farfado da zamantakewar yankin ba har ma don farfado da sana'o'in hannu.

"Bikin, wanda ake yi duk shekara abin maraba ne. Yana karfafa zamantakewa dainganta zaman tare da kuma farfado da tattalin arzikin kasar. Muna farin cikin cewa wannan biki na shekara ya dawo da karfinsa bayan da aka shafe fiye da shekara 10 ba yi ba," kamar yadda Mista Koita ya kara da cewa.

Wata kungiyar masu raye-raye suna cashewa a wajen bikin al'adar na 2023 Mopti Artistic and Cultural Biennial na 2023. Photo: TRT Afrika

Narkakkiyar tukunya

A shekarar 1970 ne aka fara gudanar da bikin mai cike da kawa na Al'adu da Wasanni, a birnin Bamako, da kuma wasu bukukuwan hudu da suka biyo bayan wannan da kuma Bikin Wasanni na 1979 a Ségou.

A kasa mai dumbin al'adu, bikin na nuna muhimman al'adunta ta hanyar raye-raye da wake-wake da zayyana da adabi tare da bai wa mutane damar bayyana fasaharsu.

Bikin na shekara tamkar wata narkakkiyar tukunya ce da ta kunshi abubuwa da dama kamar zayyana da salon rayuwa da nishadantar da mahalarta da wake-wake na fannoni daban-daban kamar Balafon daga Sikasso da Takamba da Gao da kuma Djandjigui daga Ségou.

Wata mawakiya Hawa Tapo tana ganin taron Bikin Al'ada na Biennial na Mopti na 2023 a matsayin wata alama ta dorewar zaman lafiya a tsakanin 'yan Mali.

"Na gabatar da wakoki da dama a kan zaman lafiya kuma labaraina suna kira ne ga 'alummar Mali da su zauna lafiya da juna ta yadda kwanciyar hankali za ta dawo. Mali daya kawai muke da ita kuma ya rage namu mu kula da kasarmu," kamar yadda Hawa Tapo ta shaida wa TRT Afrika.

Wasu mahalarta a wajen taron bikin al'ada na Mopti Artistic and Cultural Biennial na 2023. Photo: TRT Afrika

A kowace shekara tawagogi daga yankuna 19 da kuma gundumar Bamako ne suke yin gasa a fannoni daban-daban da suka hada da rawar gargajiya da wasannin dabe da wake-wake da sauran su.

Gasannin da suka fi wahala a kan hada su da abubuwan raha da nishadin da za su tsaya a rai.

"Ba za mu taba mantawa da bikin Arts and Culture Biennial na bana ba. Duk da tarin matsalolin da Mali ke fuskanta, matasan Mali sun yi tururuwa zuwa Mopti don halartar taron da baje basirarsu, kuma sun yi nasara," in ji Mista Koita.

Abin da a baya muke gani a matsayin wanda ba zai yiwu ba, ya zama zahiri don taron ya cika ya batse.

Mutane sun sha shagalinsu a wajen bikin al'adar. Photo: TRT Afrika

Ga alama taron Mopti Artistic and Cultural Biennial na 2023 alama ce ta dauwamar zaman lafiya da hadin kai a tsakanin 'yan Mali.

Za a yi bikin taron na gaba ne a birnin Timbuktu a shekarar 2025.

TRT Afrika