Daga Zeynep Conkar
A duniyar da karfafa gwiwa da goyon baya ke zama bisa sharudda, wasu 'yan kadan da ba a san su ba na yin hakan, suna nuna bajinta, suna magance matsala mai muhimmanci ta karfafar al'umma. Irin wadannan alheran ne ke sanya duniya na zagayawa.
A Turkiyya, sadaukarwa al'ada ce da ta samo asali daga Daular Usmaniyya, kuma tana karfafuwa ta hanyar 'rataye simit'.
A wannan makala, na yi kokarin binciko hanyoyin da mutane gama-gari suke amfani da simit a matsayin hanyar sadaukarwarsu a kowacce rana. Amma kafin hakan, bari mu ga yadda abun yake aiki.
Simit a rataye
Da fari dai, kwastoma na zuwa wajen gasa burodi ko wajen mai sayarwa a kan titi ya sayi simit - wani nau'in burodin Turkiyya na gargajiya da ake barbade shi da kantu - su nemi su biya kudin da yawa, ba tare da sun bayyana wa za a bai wa ba. Sannan sai mai gasa burodin ko mai tallan sa ya ajiye su a gefe yana sauraro.
Wani da ke cikin yanayin bukata, wanda ba shi da halin sayen abinci a wannan lokaci, zai iya iya ziyartar gidan burodin tare da tambayar ko akwai simit a rataye. Za su iya karbar simit din da wani mai sadakarwa ya riga ya biya kudinsa.
A matsayin misalin tausayawada kyautayi da karfafa gwiwa, simit na bayar da dama ga mutanen da ke cikin damuwa su samu abin ci cikin girmamawa da ladabi.
Akwai hanyoyi da dama da ake yin sadaukarwa da kyautayi a fadin kasar Turkiyya, da suka hada da sayen kayayyaki da ayyuka, kamar abinci da gahwada litattafai da tufafi da sauran su.
Wannan al'ada da ta samo asali daga Daular Usmaniyya, na ci gaba har a zamanin yau a Turkiyya, inda gidajen gasa burodi da dama da masu sayar da simit a kan tituna suke ci gaba da dabbaka wannan al'ada.
Aikata alheri
"Iyalina da ni kaina na yin wannan sana'a tsawon shekaru 11. Wasu mutane na zuwa nan su rataya simit, mu kuma muna rarraba wa marasa karfi da suke bukata, wadanda ba za su iya sayen abinci ba," in ji Demir.
Ta kara da cewa "Muna gwagwarmaya don taimakon dalibai da dattijai marasa karfi."
Demir ta kuma ce yawan simit din da ake ratayewa na bambanta a kowacce rana, daga goma zuwa 50. "Muna da masu ratayewa kullum, wasu duk mako. Misali akwai wani dattijo da ba shi da iyali, muna kai masa simit biyar ko shida a kowacce rana."
Ta ce "Gaskiya na yi amanna cewar bayar da kayan abinci sadaka kamar simit babban aikin ibada ne."
Akwai wasu misalai na wannan al'ada, a wannan lokaci kawai, ana rataye burodi ne, shi ma ya faro ne daga Uskudar.
"Al'adar rataye burodi abu ne mai matukar kyau. Wasu daga maziyartanmu na zuwa sau biyu ko uku a kowacce rana. Sakamakon haka, mun san mutane da dama," in ji Mukhamedova.
Ta ce musamman ma a ranar Juma'a, ana barin burodi da yawa a kalla guda 200 a rateye yana ta lilo, saboda rana ce ta addini ga Musulmai.
Ta kara da cewa "Wasu mutanen na barin burodi 30 zuwa 50 a lokaci guda. Adadin na iya raguwa a wasu ranakun, ba ma taba hana wani karba, ko da za mu yi asara ne a ranar."
Ta ci gaba da cewa "Na yi amanna cewa ta hanyar aikata alheri ga wasu mutanen, muna amfanarwa ba ga su kadai ba, har ma ga kawunanmu. Ina fatan wannan kyautatawa za ta isa ga kowa."
Asali daga Musulunci
A Turkiyya, taimakon jama'a abu ne da ake hada kai a gudanar da shi. A al'adar da aka samar a tsakanin jama'a, ga su da karfafa gwiwa ga karamci, mutum zai iya tsinkaye irin wannan abu a ko yaushe.
Kamar Yadda Annabi Muhammad ya fada "Ba shi da imani, duk wanda ya ci ya koshi, amma makocinsa ya kwana da yunwa."
Aikin alheri - wanda aka yi wa makota ko baki - na da muhimmanci a Musulunci, kuma kyakkyawar zuciya ce ke damuwa da aikata alheri ga wasu.
Misalan irin wannan aiki na alheri da karfafa gwiwa na da yawa a lokutan bukukuwa ko makoki. Taron jama'a na kulla dankon zumunci mai dorewa, kamar yadda taimako mai tasiri ke hade zukata waje guda don manufar da za ta amfani kowa.
A watan Ramadhan mai girma da daraja a wajen Musulmai, ana yawaita aikata alheri.
Musulmai na yawan raba abincinsu tare da wadanda suke cikin halin bukata a lokutan sahur da buda-baki, hakan na kara karfafa taimakon juna a Turkiyya.
Annabi Muhammad SAW ya kuma ce "Mafiya alheri daga cikinku su ne wadanda suka fi amfanar da wasunsu." A Musulunci, aikata alheri, biyan bukatar wadanda ke cikin mawuyacin hali da bayar da abun da kuke da shi ga mabukata, abu ne da ake yi a ko yaushe.
Dabi'un Musulunci na kyautayi da hidimtawa wasu, suna nan cakude da al'adun Turkawa na sadaukarwa da taimakon juna da suke yi na zakka da aka wajabta da kuma sadaka ta neman karin lada.
A aya ta 271 ta Suratul Bakarah (2:271) a Alkur'ani Mai Tsarki Allah SWT ya ce "Idan kun nuna sadakoki to, yana da kyau ƙwarai kuma idan kuka ɓoye su kuma kuka je da su ga matalauta, to shi ne mafi alheri a gareku, kuma hakan zai kankare muku wasu zunubanku. Allah Masani ne ga dukkan abubuwan da kuke aikatawa."
Wannan shi ne abun da littafi Mai Tsarki ya koyar game da bayar da sadaka, tare da kare duk wata kafa ta tozartarwa ko kunyata wanda ake baiwa.
Kyautar murmushi ga yara kanana
Ahmet Ersan da aka fi sani da 'Cakir Ahmet na Uskudar' wani mai sayar da carbi ne a kan titi. A gaban dan kes dinsa, yana neman mutane da su rataye burodi, shi kuma ya ba su carbinsa.
A matsayin sananne kuma da ake kauna sosai, idan abokaina za su ziyarce ni, za su ajiye karin kudi a teburina, su ce na rike sauran canjin. Sai na yi amfani da kudin wajen taimakon mabukata, musamman ma yara kanana. Ta yadda lamarin ya faro kenan," in Cakir AHmet.
Cakir Ahmet ya ce "Na saba ina raba wa yara kanana da dalibai kayan ciye-ciye. Ina jin dadi idan na ga suna farin ciki, kuma tunanin aikata alheri abu ne mai kyau sosai. Za ka bai wa yaro alawa, za su tuna wannan abu har abada."
Ya bayyana wani labari da ba za a manta da shi ba da cewa "A lokacin da nake kamar dan shekara takwas, ina sayar da jarida. Wata rana wani mutum ya kusanto ni ya tambaye ni ko ina jin yunwa. Sai ya saya min doner mai nama. Da ya lura ina sanye da tsohon takalmi, sai ya kai ni wani shago tare da saya min takalmi da kilo guda na kayan marmari. Wannan kusan shekara 60 kenan, amma har yanzu ina iya tunawa da wannan lokaci."
Ya kara da cewa "Yara kanana ba sa mantuwa da wuri. A lokacin da suka girma, za su iya tunanin: 'wani ya yi mana alheri wata rana, to ni ma sai na aikata irin wannan alheri ga mabukata ko yara kanana'.
"Mun dukufa wajen dabbaka wadannan al'adu. Game da ni, ina raba alawa ga yara kanana da wadanda ba su da gidajen zama."
"Wasu masu ziyarta mako-mako na ajiye kudade kuma su bayyana cewa 'Ahmet, ka san me za ka yi'. Sai na rataye kayan zakin don raba wa yara kanana daga baya."
A gidan kula da yara da ke unguwar Balat a Istanbul, wanda aka kafa don taimakon yara kanana marasa galihu, akwai wajen rataye kayan sa wa da ba a amfani da su kuma ake so a bayar da su kyauta. Mutanen da ke zuwa wajen na zabar kayan da za su yi musu daidai, su tafi da su gida.
Abincin ruhi
Waye ya ce wadannan ayyuka na alheri na amfanar masu karba ne kawai? Misali irin wadannan ayyuka na alheri na ciyar da ruhin mai bayar da kyauta da sadaka ne.
Irin wadannan ayyuka na alheri da kyautayi na rayar da insaniyya, yana tunatar da mai bayarwa cewa aikin alherin na iya yin tasiri mai kyau a rayuwar wanda yake taimakawa.
Haka kuma an san ayyukan alherin da sanya wadatuwa. Sannan sanin cewa suna magance wata wahala da ke damun wani, na sanya musu gamsuwa da wadatuwa, hakan na kara inganta lafiyarsu.
Asali dai, a yayin da 'suke a rataye', wannan al'ada na dabbaka yadda taimakon juna yake tare da tausayi, sannan hakan na bayyana karfin tausayi a aikace da a cikin zukata.
Ta wannan hanya, al'adar Daular Usmaniyya na ci gaba da wanzuwa a yau a Turkiyya, a cikin sirri ba tare da ana ankarewa ba, amma kuma tana bayar da gudunmawa sosai waje kawo sauyi a bangaren cimaka.