Daga Kudra Maliro
Hotuna da sauti cikin karsashi na shagulgulan tsawon mako biyu suna kawo hada-hada a garin Bonoua.
Garin Bonoua yana da nisan kilomita 50 daga gabashin birnin Abidjan, wato babbar cibiyar tattalin arzikin kasar Côte d'Ivoire.
Ana rera wakoki yayin shagulgulan Popo da raye-raye, kuma ana sanya kayayyakin al'ada masu daukar hankali. Bikin ya samo asali ne daga bikin girbin doya na kabilar Aboure na Bonoua a shekarar 1946.
Zamanin matasan wadanda yanzu sun zama manya suna kaunar shagulgulan "Popo Carnival," inda aka zamanantar da shi da gwauraya shi da wasu shagulgulan al'adu ciki har da fareti daga wasu kabilu da ke kasashen yankin Yammacin Afirka.
Popo yana nufin " takunkumin fuska" a harshen Aboure.
Shagulgulan suna zama wani bangare na al'adar kabilar Aboure a shekarar 1972, wadanda ake yi a duk shekara lokacin bikin Easter a watan Afrilu, inda ake zuwa daga sassa daban-daban.
A wata tattaunawa da TRT Afrika, Junior Kouassi, sakataren yada labaran Shagulgulan Popo, ya ce suna fatan bikin Popo na Bonoua ya yi gogayya da Bikin Al'adu na Rio de Janeiro wanda mutum kusan miliyan biyu ke halarta.
"A shekarar 2023, mutum kusan dubu bakwai ne suka ne halarta a tsawon mako biyu, kuma fatanmu shi ne yabyi gogayya babban bikin al'adu na duniya. Manufar ita ce mu koya kuma yi irin yadda suke yi, kuma mu kara kawo abubuwan al'adu da tallata al'adu da dabi'u da kuma wayar da kan jama'a kan al'adun mutanen Aboure," in ji Kouassi.
Garin Bonoua ya karbi bakuncin tawaga daga Brazil da Trinidad and Tobago yayin bikin na wannan shekarar.
Kabilar Aboure, kamar sauran kabilu a Côte d'Ivoire suna da sarki da sarauniya wadanda suke taka muhimmiyar rawa a al'adance.
"Daya daga cikin manyan abubuwan da ake yi yayin shagulgulan shi ne fareti bayan isowar sarki wanda yake sanya hular zinare da doguwar alkebba. Ana raka sarkin ana buga ganga da bushe-bushen kaho," in ji Mista Kouassi.
Ana kuma buga wasan kwallon kafa da sauran wasanni da gasar girke-girke da gasar sarauniyar kyau da sauran abubuwa a wani bangare na shagulgulan al'adar Popo.
Dalilin yin shagulgulan shi ne raya al'adun kabilar Aboure da kuma tuna musu abin da suka rasa da kuma wanda suka yi nasara.
"Lokaci ne na yin nazari don duba ko akwai wani abu da muka rasa da iyayenmu suka bar mana," in ji Kouassi.
Kamar yadda wadanda suka shirya bikin suka bayyana samar da wani kauye da ya hada kowa da kowa wani sabon abu ne da aka kirkiro a yayin bikin na bana.