Daga Charles Mgbolu
Bukin Nuna Fina-Finan Afirka na 2023 (AFRIFF) ya sake gabatar da dama ga kwararrun da ke wannan masana'anta don su taru su yi bukin shekarar fim da musayar ra'ayoyi.!
Bukin karo na 11 da aka gudanar tsakanin 5 da 11 ga Oktoba a birnin Legas na Nijeriya, ya samu mahalarta mutane daga ciki da wajen Afirka.
Bukin na wannan shekarar na fatan gano sabbin dabaru, kirkirar damarmaki da nuna daruruwan fina-finai kyauta, in ji jami'ar hulda da kafafan yada labarai ta AFRIFF, Latasha Ngwube yayin bayani ga mahalarta bukin.
Ta ce "Duniya na zuwa Nijeriya a yayin da AFRIFF ke kokarin karfafa yadda za a kai fina-finan Afirka zuwa sauran sassan duniya."
Bukin ya samu tarurruka tare da masu da ke musayar ilimi da hikima, alakar samar da fina-finai da dnagantakar kasuwanci da ke kara daraja, gina kokari da samar da kudade.
Masu shirya bukin sun kuma bayyana cewa taron zai bayyana inda ake da rauni da kuma damarmaki.
Wasu daga cikin manyan masu jawabi da alkalai sun hada da sanannen mai shirya fina-finai na Sanagal Boye Pape, mai rubuta labari dan kasar Zimbabwe Tsotsi Dangarembga, da babbar jaruma 'yar Nijeriya Kate Henshaw.
Masu shirya fina-finai daga sama da kasashen duniya 150 ne suka mika fina-finansu don tantancewa a wannan shekarar, in ji masu shirya bukin.
Za a karkare bukin na AFRIFF da sanar da wadanda suka samu kyauttukan kasa da kasa.
Bukin na bana zai kuma bayyana sabbin bangarori uku, wanda suka hada da Kambin Honoree, Zabin Masu Kallo, baiwa masu kallo damar yin zaben jaruman da suka fi kauna,
A daren 11 ga Nuwamba din nan ake rarraba kyaututtuka da kambi ga wadanda suka yi nasara.