Daga
Charles Mgbolu
Magoya bayan tawagar mawaka salon Afropop Sauti Sol suna shirin yin wasan bankwana mai sosa rai yayin da suka fara yin wasanni karshe a nahiyar Afirka da sauran sassan duniya.
A watan Mayun 2023 ne tawagar mawakan Sauti Sol ta sanar da rabuwa bayan shekara 18 da suka kasance a tare kuma yanzu mambobin tawagar kowane zai fara cin gashin kansa, bayan sun kammala wasannin bankwana da aka shirya yi a ranar 2 ga watan Nuwamban bana a birnin Nairobi.
Kodayake tikitin wasan ya samu kasuwa sosai a intanet da kuma a wajen intanet, inda magoya bayansu da dama suke mamakin tsadar tikitin.
Babban tikitin ana sayar da shi ne kan Shilling na Kenya 20,000 (dala 138 kenan), kamar yadda wadanda suka shirya wasan suka bayyana, wanda suka kawata tikitin da wasu kyautuka.
Babban tikitin ya kunshi liyafa da abubuwan sha da ganawa da mawakan Sauti Sol da uwa uba kallon wasansu kai-tsaye.
Tawagar ta yi alkawarin yin gagarumin wasa, inda ta ce "Wannan ba karshen tawagar ba kenan, amma wannan ne matakin farko na babban aikinmu wanda ba zai taba goguwa ba a zukatan magoya bayanmu ba."
Sai dai farashin tikitin ya sa magoya bayansu da dama ba za su iya halartar wasan ba.
‘’Bai kamata ku yi mana haka ba," kamar yadda wani magoyin bayansu @terrylnemboya ya bayyana a shafin X, wanda a baya ake kira Twitter.
‘’Sai dai na leka ta katanga don na kalli wasan," kamar yadda wani mai sha'awar wakarsu @reccro ya bayyana a shafin X.
Wasu sun ja hankalin tawagar dangane da halin matsin rayuwa da ake ciki a Kenya, yayin da wasu suke cewa wata kila tawagar ta yi abin da ba a zata ba.
Duk da sukar da ake wa tawagar, masu sha'awar wakokinsu da yawa suna kare su, ciki har da mawaki kuma marubucin wakoki Bensoul.
"Idan ba za ka iya tara shilling 20,000 daga nan zuwa watan Nuwamba ba, to lalle kana da aiki a gabanka. Ku bari mu da muke da wadata mu je kallon wasan saboda za mu iya zuwa babu fashi," kamar yadda ya bayyana a shafinsa na X.
Sakonsa ya jawo ce-ce-ku-ce daga magoya bayan mawakan, abin da ya sa wasu daga cikin mambobin tawagar Sauti Sol Bien Aime Baraza da kuma Savara Mudigi suka yi magana kan batun.
A wasu jerin ganawa da manema labarai, mawakan sun jaddada dacewar farashin.
"Za mu ba ku shekaru 20 ne na rayuwarmu, mun kasance tare tsawon shekaru 20. Tikitin yana da darajar shekara 20 da muka kasance tare ne," in ji Bien.
Savara ya ce farashin tikitin yana nuni da tsadar rayuwa da kuma tsadar shirya wasan.
"Kudin da aka kashe wajen shirya wasan suna da yawa. Ba wai muna so ne mu cuci mutane ba ne," in ji Savara.
Tawagar ta kuma ce tana so ne za ta yi wa magoya bayanta kayataccen wasa.
Ana ci gaba da muhawara kan farashin tikitin wanda ya raba kan magoya bayansu, inda wasu masu mutuwar son wakokinsu suka ce ko ana ha maza, ha mata, sai sun biya kudin tikitin sun kalli wasan.
Masu fashin baki kan kade-kade da wakoki sun ce za a sayar da duka tikitin kafin wasan, inda aka sayar da kananan tikitin da ake sayarwa shillings 2,500 gaba dayansa wata guda bayan fara sayar da shi.