Saidu Abdulrahman, mai shekara 28, ɗan Nijeriya daga jihar Yobe da ke ɗaukar hoto, ya lashe kambin lambar yabo ta 'Guinness World Records' (GWR) a hukumance, a matsayin wanda ya fi ɗaukar hotuna kai-tsaye cikin sa’a guda.
A cikin mintuna 60 kacal Abdulrahman ya ɗauki hotuna 897 masu jan hankali a watan Satumban 2024, hakan ya ba shi damar kafa tarihin doke wanda ya lashe kambin a bara da hotuna 500.
"Ina mai farin cikin sanar da cewa, an karrama ni a hukumance da matsayin mai riƙe da kambin tarihi na Guinness saboda na mafi ɗaukar hotunan da yawa waɗanda na ɗauka cikin sa'a ɗaya!" kamar yadda Abdulrahman ya bayyana a wani saƙon Facebook da ya wallafa.
Abdulrahaman ya yi yunƙurin kafa tarihin ne domin wayar da kan jama’a game da ɗaukar hoto a Nijeriya, in ji GWR a cikin wata sanarwa da ta fitar.
Shirye-shirye na tsawon shekara guda
An ba shi lambar yabon ne a garin Potiskum da ke jihar Yobe, kana taron ya samun halartar jami'an gwamnatin jihar da ɗalibai da kuma masoyansa.
Taron dai ya kawo ƙarshen shirin tsawon shekara guda da Abdulrahman ya yi na samun wanna dama.

Ko da yake an gudanar da gasar ne a watan Satumba, amma sai daga baya ne Abdulrahman ya sami tabbaci a hukumance daga Guinness World Records ta saƙon imel.
An kuma bashi takardar shaida da kuma lambar yabo ta bajinta.
"Karɓar shaidar lashe lambar yabo ta kudin Guinness World Records, sakamako ne na jajircewa ta da kuma goyon baya mara iyaka daga dangina da abokaina, da jagororina, da masu yi min fatan alkhairi waɗanda suka kasance tare da ni," kamar yadda Abdulrahman ya wallafa.
Ya sadaukar da wannan nasarar da ya samu ga duka 'yan Nijeriya, yana jaddada cewa jajircewa na kai mutum samun yabo a duniya.
'Ba tawa ce ni kaɗai ba'
Ya ce "Nasarar kafa wannan tarihi na ɗaukar hotuna 897 a cikin minti 60 kacal, ba tawa ce ni kaɗai ba; ta duk ɗan Nijeriya ce da ya amince da ni, ya taimaka min, ya kuma jinjina min tun daga lokacin da na fara har gama."
"Kafa wannan tarihi shida ne na cewa za mu iya yin bajinta a duniya."
Nasarar Abdurrahman wata shaida ce ta irin yadda 'yan Nijeriya suka dagewa da ƙoƙarin ganin duniya ta san irin abubuwan da suke yi.