Duk da cewa kusan ko'ina akwai makana ta latironi, amma ga wasu mutane sun fi jin dadi idan aka yi musu aski da askar wanzamai.
Wanzamai suna gudanar da sana’arsu a yanayi mai sauki inda masu son aski za su zauna kan kujeru ko kuma kan tabarma a waje.
Malam Ibrahim, wani mutum da ke jihar Zamfara a arewa maso yammacin Nijeriya, na cikin mutanen da ba za su iya daina aski a wurin wanzaman gargajiya ba.
“Aski a wurin wanzaman gargajiya yana da kyau domin za a aske kaina tal kuma ba zan samu amosanin kai ba kamar yadda nake samu idan na yi aski da makana ta laturoni,” in ji shi a hirarsa da TRT Afrika.
“Ina samun kuraje a kaina duk lokacin da na yi amfani da makana wajen aski. Amma idan aka yi amfani da askar wanzamai ba zan samu wata matsala ba,” a cewarsa.
Kazalika masu yin aski a wurin wanzamai na bayyana cewa suna yin aski a wurinsu ne saboda hakan yana rage kasadar kamuwa da cutar fata a kai.
Rabiu Adamu yana cikin wadanda ke da irin wannan ra'ayi.
“Akwai lokutan da za ka ji kanka na ciwo. Idan wanzami ya yi maka aski, wannan zai ba ka damar shafa kanwa da aka hada da lemon tsami a kan naka,” a cewar Rabiu, wanda ke zaune a jihar Katsina, a hirarsa da TRT Afrika.
Ya kara da cewa shi ya fi son askin wanzamai ne saboda masu askin na gargajiya suna yi masa irin askin da ke ba shi damar shafa magani a kansa.
“Duk da cewa ina jin zafi, amma ina yin hakuri har ya daina. Sannan za mu wanke shi. Bayan kwanaki kadan ciwon kan zai tafi,” in ji shi.
Tsoron cuta
Sukar da aka dade ana yi wa masu askin gargajiya ita ce amfani da aska daya kan mutane daban-daban, lamarin da ka iya yada cuta idan ba tsaftace askar ba.
“Ba na tsoron wannan (kamuwa da cuta ta askar wanzami) saboda
A ganinsa, Rabiu ya ce duk da cewa ba shi da tabbacin sahihancin matakin da wanzamai ke dauka game da tsare lafiyar mutane daga kamuwa da cututtuka, zai ci gaba da yin aski a wurin ma'askan gargajiya.