Daga Mazhun Idris
Balaraba Ramat Yakubu tana 'yar shekara 12 aka cire ta daga makaranta, sannan aka mata aure, amma sai auren ya mutu bayan shekara biyu.
Ba tare da yin kasa a gwiwa ba, Balaraba ta ceto rayuwarta ta hanyar komawa makaranta. Daga nan ta shiga harkar rubuce-rubuce, har ta zama shahararriyar marubuciyar kagaggun labarai, kuma mai fafutukar ci-gaban mata a Arewacin Nijeriya.
Lokacin da ta rubuta littafinta na farko a shekarar 1987, ita ce ta uku a mata marubutan Hausa a yankin, kuma ta biyu da ta wallafa littafi cikin daya daga cikin manyan harsunan Afirka.
An haifi Balaraba a shekarar 1958 a garin Kano na Nijeriya, daga inda ta zamo gagarumar gwarzuwar da ta rubuta littafai har 10.
Ita ce mafi shahara cikin mata marubutan Hausa masu rubutu a fannin littafan soyayya, inda da ma yawancin marubutan mata ne.
Balaraba ta fada wa TRT Afrika cewa, "A shekarar 1996, biyu daga cikin litattafaina, wato "Budurwar Zuciya" da "Wa Zai Auri Jahila?", sun shiga sahun littattafan da Novian Whitsitt na Jami'ar Wisconsin-Madison, ya nazarta a karatunsa na digirin digirgir".
Dr Whitsitt kuma ya nazarci littafan Bilkisu Funtua, ita ma wata babbar marubuciya.
Marubuciya da ta bude hanya
A tarihin al'ummar Hausa, mata sun yi rubuce-rubuce da harshen Hausa a fannin addini da wakoki, ta amfani da haruffan Larabci. Amma a fannin rubutun adabi, har da na mata, ana yada ilimi ne ta labarin baka, wadanda aka taskace kuma ake bayarwa cikin Tatsuniyoyi.
Balaraba mrubuciya ce da ta ciri tuta, kuma ta fada wa TRT Afrika cewa, "Ni ce mace daya kacal a cikin marubuta bakwai da suka kafa kungiyar farko ta marubutan adabin Hausa a Kano, wato kungiyar "Raina Kama", wadda aka kafa a shekarun 1980."
Ma'anar sunan kungiyar shi ne, "abin da ka raina zai iya shige tunaninka", wanda ke nuna kokarin da matasan marubutan wancan lokacin suka yi, wadanda suka assasa fagen kagaggen rubuce-rubucen Hausa, da tasirin su kan ginuwar harkar fim da wake-waken Hausa.
Lokacin da mata marubuta Hausa suka kara yawaita, Balaraba ta kafa kungiyar marubuta mata zalla mai suna, "Kallabi Writers", a watan Yuli na shekarar 2008. Kungiyar ta fara da mambobi 38, yawancinsu daga Kano, inda Balaraba take da matsayin uwa ma-ba-da-mama a wajen marubuta.
Ta fada wa TRT Afrika cewa, "Har zuwa yau, matasan marubuta Hausa da dama suna ta'allaka shigarsu harka da ni. Ana yawan tuntuba ta don na bayar da shawarwari a fannin rubutun labarin fim, da tace fim, da sharhi kan fina-finai. Na samu nasarori da dama."
A shekarar 2012, wani kamfanin wallafa littafai na Indiya mai suna Blaft Publications, ya wallafa fassarar Ingilishi na littafin Balaraba, wato "Alhaki Kwikwiyo (da sunan "Sin is a Puppy That Follows You Home"). Hakan ya sanya littattafanta sun kara samun yaduwa a fadin duniya.
Shiga harkar fim
Hajiya Balaraba tana zama a garin Kano, wanda shi ne cibiyar gwamin al'adun Hausa, da kasuwanci, da kuma rubutu da wallafa littattafan adabin Hausa da na addini. Kano ce cibiyar fina-finan Hausa, kuma ana kiran masana'antar da sunan garin, wato Kannywood.
A shekarar 1999, an nemi amincewar Balaraba don a mayar da littafinta na "Alhaki Kwikwiyo" zuwa fim. Amma sai ta zabi ta zama mai kula da suturar 'yan wasan, domin ta tabbatar fim din ya dace da labarin littafin. Daga nan ne ta samu azamar shiga harkar fin din Hausa a matsayin marubuciyar labarin fim.
Ta bayyanawa TRT Afrika cewa, "Ni na rubuta labarin fim din "Wata Shari'ar Sai a Lahira", wanda ya ci kyautuka a Bikin Bayar da Kyautuka na kungiyar "Motion Pictures Producers Association of Nigeria's Millennium Awards".
Wasu fina-finan Hausa da Balaraba ta shirya sun hada da "Ina Sonsa Haka" da gagarumin fim din nan na "Juyin Sarauta ", wanda ya ci kyautuka sama da 10.
Mata a fagen adabin Hausa
Maimuna Beli, wata babbar marubuciya ce kuma mataimakiyar shugaban Kungiyar Marubutan Nijeriya ta "Association of Nigerian Authors", reshen jihar Kano. Tana ganin cewa kasancewar mata a al'ummar Hausa suna rayuwa ne a cikin gida, hakan yana ba su lokacin karatu, wanda shi kuma yake ba su "kwarin gwiwar yin rubuce-rubuce".
Bisa dabi'a mata suna da kaifin basira a fannin koyo da koyarwa, ta inda suke iya tara ilimi da kwarewa. Yayin da suka yi rubutu, suna iya sawwara wata nau'in duniya mai cika burinsu da fatansu.
Baya ga haka, ga matan arewacin Nijeriya, rubutu sana'a ce da ake yi daga gida, kuma tana taimakawa wajen samar da kudin shiga gare su, yayin da kuma take ba su damar yin ayyukansu na kula da gida.
Labarin rayuwar Balaraba cike yake da darasi kan yadda jajircewa ta kai ta ga nasara, duk da ta samu cikas a farkon rayuwarta saboda rashin yin karatu.
Maimuna ta ce, "Mata marubuta da yawa sun dauki rubutu a matsayin hanyar nuna rashin adalcin da ake musu, da kuma sauya rayuwarsa mara armashi zuwa wata kagaggiyar rayuwa mai cika burinsu.
"Akwai gamsuwa idan kika iya zube damuwarki a takarda. Mata suna son rubutu, saboda kusan babu wanda yake sauraron su ko yake amanna da abin da suka ce."
Yayin da take da shekaru sama da 60 a duniya, Balaraba tana ayyukan ba da shawarar kwararru a gidauniyar da aka kafa don yayanta, tsohon shugaban mulkin soja na Nijeriya, marigayi Janar Murtala Ramat Muhammad, wanda ya rasu a shekarar 1975.