Daga Abdulwasiu Hassan
Dogarai suna daga cikin mutane masu muhimmanci a masarautu a faɗin duniya, inda suke da biyayya da kuma yin iya bakin ƙoƙarinsu domin bai wa masarauta kariya.
Irin dogaran da ake gani suna rakiya ga sarakai a arewacin Nijeriya, suna sanye da korayen tufafi da jan rawani, inda hakan ke nuni da wata al'ada wadda aka shafe ɗumbin shekaru a kanta.
Dogaran sarki sun wuce masu gadin sarki. Suna kasancewa waɗanda amanar gidan sarautar Hausa ke ƙarƙashinsu, inda suke tabbatar da cewa ana bin tsari wurin yadda ake ganin sarki da girmama shi.
A cikin fada ko a wurin wani taro, mawuyacin lamari ne mutum bai ci karo da su ba sakamakon irin tufafin da suke sakawa da kuma aiki ba kakkautawa - wanda ya haɗa da sunkuyawa gaban sarki zuwa ga yi masa kirari da kuma ɗaga babbar rigarsu domin kare shi idan zai yi wasu abubuwa kamar shan ruwa ko zama domin kada al'umma su gan shi.
Kasancewa tare da sarki a kowane lokaci
Ana ɗaukar dogari ne domin ya yi aiki har ƙarshen rayuwarsa inda kuma yake rayuwa a wani wuri na musamman a fadar sarki.
Duk da cewa muhimmin aikinsu shi ne samar da zaman lafiya da tsaro a gidan sarki, tasirin dogaran ya wuce cikin fadar sarki inda ya fita zuwa waje a zamanin baya, musamman lokutan da Nijeriya ta kama hanyar samun 'yancin kai.
Nasir Wada Khalil, wanda ƙwararre ne dangane da tarihi kan dogarai ya yi rubutu kan yadda waɗannan masu kula da fadar suke — da yadda sunansu ya samo asali daga kalmar "dogari".
Sarkin dogarai ne ke jagorantar dogarai a kowace fada.
"Su ke da alhakin sinitiri da kula da fadar sarki da kama duk wani da aka kama da aikata laifi a cikin fada. Su ne kuma masu kula da sarki, inda suke tabbatar da lafiyarsa da kula da shi idan an fita waje wurin wani taro," kamar yadda Khalil ya shaida wa TRT Afrika.
Ɗaukar aiki a hukumance
A shekarar 1909, a zamanin mulkin Sarkin Kano Abbas, dogarai 283 ne aka saka sunansu domin a rinƙa biyansu albashi. Wannan wani muhimmin mataki ne wanda ya nuna aminta da aikin da suke yi a fada.
Haka kuma Abbas ɗin ne ya kawo irin wannan tufafin nasu da suke sakawa a halin yanzu.
"Launin ja alama ce da ke nuna ƙarfin mulki sai kuma tsanwa alama ce da ke nuna wadata. Waɗannan na daga cikin abubuwan da ake buƙata domin gudanar da mulki," kamar yadda Khalil ya yi ƙarin bayani.
Soma amfani da tufafin dogarai ko da aka soma kawo kudirin ya fuskanci turjiya.
Sai da sarkin da kansa ya saka kayan kafin dogaran suka samu ƙwarin gwiwar sakawa.
Ayyuka masu sauyawa
A daidai lokacin da Kano ke ƙara haɓaka, wasu daga cikin dogaran sai aka saka su domin kula da harkokin cikin gida.
"Zuwa shekarar 1925, sai faɗaɗar masarautar ta ƙara kawo ƙalubale ga bin dokoki, wanda hakan ya sa aka ƙara yi wa ayyukan na dogarai kwaskwarima," kamar yadda Khalil ya bayyana. "An zaɓi kusan 200 daga cikinsu domin a ba su horo don su kula da cunkoson ababen hawa da wasu."
A yau, tufafin nasu yana kama da na dogaran Kano da na sauran dogaran ƙasashen Hausa.
Duk da aikinsu na gargajiya, waɗannan dogaran an yi musu horo na musaman domin tunkarar duk wata barazana da za ta iya kunno kai.