Ayyukan ƙwararrun masana fasaha daga Kano da jihohi maƙota. / Hoto: Kabara Gallery/Ad Visuals

Daga Mazhun Idris

Wani zauren nune-nune mai zaman-kansa da ke jihar Kano a arewacin Nijeriya ya gudanar da bikin nune-nune da ke bayyana ayyukan sassaƙar itace da ƙere-ƙeren ƙarfe da tagulla. Bikin ya ƙayatar da waɗanda suka je kallo matuƙa.

Bikin nune-nunen ya gudana ne a farkon watan Maris kuma shi ne karo na biyu da Kabara Kreative tare da hadin gwiwar Society of Nigerian Artists da Hausa Art Studio da Bakale Arts & Crafts da Herwa Heart of Art da FLINT da kuma poetic Echoes suka shirya.

An nuna ayyukan masu fasaha kimanin goma sha biyu, kuma shirin ya samu halartar masu sha'awar fasaha da ƙwararrun masu fasaha daga ciki da wajen kewayen birnin Kano mai daɗɗaɗen tarihi.

Hoton Sassakar itace mai suna "The Couple" na  Habibu Rabiu. / Hoto: Zauren nune-nune na Kabara Gallery/Ad Visuals

Ayyukan da aka nuna sun haɗa da fasahar "The Village" na Fatima Zakari, sai "The Couple" da "Nest" na Habibu Rabiu da "Delilah," da kuma "Aesthetics," da "Biomorphic Portrait," da kuma "City (na Habasha) of My Dreams" na Simone Ngadda.

Maryam Batool wacce ke kula da zauren nune-nunen, ta shaida wa TRT Afrika cewa taron ya shafi bikin kirkire-kirkiren fasaha da al’adu da aka samu daga al’ummar Kano.

Hoton aikin sassakar karfe mai suna "The Village" na Fatima Zakari. / Hoto: Zauren nune- nune na Kabara Gallery/Ad Visuals

"Manufarmu ita ce samar da dandamali ga masu fasaha don su iya bayyana manufarsu, su kuma gana tare da masu zuwa kallo da kuma karfafa wa sauran mutane ta hanyar ayyukan su da suke yi, " in ji Batool.

Masu kirkire-kirkiren sun haɗa da masu zane-zane da masu aikin sassaƙa, da masaƙa, yayin da kayayyakin aikin suka haɗa da yumbu da fenti da duwatsu zane-zane da itace da karafa da sauran gaurayen kayayyakin fasaha.

Hoton "Biomorphic" na Simon Ngadda. / Hoto: zauren nune-nunen fasaha na Kabara

"Akwai kyawu da fasaha da ke cikin kowane aikin da aka nuna," kamar yadda Imam Khalid, ƙwararre a fannin ƙere-ƙere a wurin taron, ya shaida wa TRT Afrika.

Aikin  Ceremic works. / Hoto: Zauren nunne-nune na Kabara Gallery/Ad Visuals

“Ba za a iya rubuta labaran da suka shafi tarihi da al’adu da yanayin kunci da ƙauna ba cikin kalmomi da littattafai kaɗai ba. A nan ne ayyukan sassaka da zane-zane suka amfanar,” a cewar Imam.

Gaurayen hadin fasaha da aka sa masa suna da "The Nest"  na  Habibu Rabiu. / Hoto: Zauren nune-nune na Kabara Gallery

Kabara Kreative, wani aiki ne na shirin ci gaban al'ummar Kabara mai zaman kansa wanda aka kafa a shekarar 2016.

Mai kula da zauren nune-nunen Batool ta ce ayyukan shirin fasahar zai taimaka wajen kara karfafa hadin gwiwa tsakanin kungiyoyin al'adu.

/ Hoto: zauren nune-nune na Kabara Gallery/Ad Visuals

"Muna goyon bayan sake farfaɗo fasaha da ayyukan fasaha da zamantakewar al'adu, sannan muna kuma son mu ƙirƙira labarun zamantakewa na kimiyya da fasaha da injiniyanci da lissafi da kuma zane," in ji Batool.

Hoton "Delilah" na Simone Ngadda. / Hoto: Zauren nune-nune na Kabara Gallery/Ad Visuals

Daya daga cikin hanyoyin da za'a bi wajen cimma hakan shi ne samarwa matasan arewa masu hazaka wani dandali da za su baje baiwarsu da kuma hanyoyin kasuwanci wa kawunansu a cikin yanayi mai aminci.

TRT Afrika