Wadanda suka shirya taron sun bayar da shawarar hade fasahohin Hausa na gargajiya da na zamani. / Hoto: HIBAF

Biki ne wanda aka gudanar wanda aka baje kolin al'adu da fasaha na Bahaushe a birnin Kano da ke arewacin Nijeriya.

Dakin taro da ke rukunin shaguna na Ado Bayero ya cika ya batse sakamakon masu fasaha da mawaka da malamai da daliban adabin Hausa wadanda suka taru domin murna da bita da kuma dabbaka al'adar Hausawa.

An gudanar da Bikin Baje Kolin Littattafai Da Fasahohin Hausawa daga 14 zuwa 16 ga watan Disamba.

Hausawa suna da kayayyakin kida iri daban-daban wadanda hakan ke kara haba al'adarsu. / Hoto: HIBAF

Babban burin HIBAF shi ne karfafa gwiwa kan tattaunawa da kirkira da kuma fahimtar harshen Hausa da al'adun Bahaushe baki daya a duniya wadda a halin yanzu take sauyawa.

An kaddamar da bikin na shekara-shekara a 2021 Jihar Kaduna da ke arewacin Nijeriya wanda kungiyar Open Arts ta assasa, wadda kungiya ce mai zaman kanta. Jigon bikin na bana shi ne "Hausawa da ke kasashen waje".

An kaddamar da bikin na shekara-shekara a 2021. / Hoto: HIBAF

A yayin bikin, "ana murna da irin al'adun da Hausawa suke da su ta hanyar gabatar da lakcoci da tattaunawa ta kan tebur da kuma shakatawa da masu fasaha na al'adun na Hausa," kamar yadda shugaban na Open Arts Sada Malumfashi ya shaida wa TRT Afrika.

Bikin Baje Kolin Littattafai Da Fasahohin Hausawa na baje-kolin al'adun Bahaushe. / Hoto: HIBAF

Bikin na fito da tarihi da kuma kyawawan al'adun Bahaushe da suka shafi baje fasahohi da raye-raye da wake-wake, da kuma game al'adun gargajiya na Bahaushe na zamanin baya da kuma na yanzu ta hanyar mazauna kasashen waje.

Wadanda suka shirya taron sun ce bikin ya tabo batun gudunmawar da Hausawa da ke kasashen waje ke bayarwa wurin kawo ci gaba ga harshen Hausa da al'adu da kuma bukatar bayar da karfin gwiwa domin hada kai da al'ummomi.

An baje-kolin zane-zane na fasaha a HIBAF a birnin Kano. / Hoto: HIBAF

An samu mahalarta taron daga kasashe dama kamar Nijar da Ghana da Kamaru da Togo da sauran kasashen Afirka. Haka kuma an samu wadanda suka halarci taron daga wajen nahiyar Afirka.

An bayar da kyaututtuka ga mutane da dama a yayin taron dangane da irin gudunmawar da suke bai wa adabin Hausa da kuma ci gaban al'adar Hausa.

Adabin Hausa ya bazu a 'yan shekarun nan zuwa jami'o'in Turai da Asia. / Hoto: HIBAF

Hausa na daga cikin harsunan da aka fi magana da su a Afirka musamman yammaci da tsakiyar nahiyar.

Jama'ar Hausa sun fi yawa a arewacin Nijeriya da Nijar inda ake da masu magana da harshen da dama a Kamaru da Ghana da Chadi da Sudan, haka kuma akwai Hausawan a Turai da kasashen Asia.

An gudanar da bikin tun daga ranar Alhamis zuwa Asabar. / Hoto:HIBAF

Kamar yadda tarihi ya nuna, Hausawa sun gaji noma kuma 'yan kasuwa ne wadanda suka ke da fasahohi daban-daban.

Baya ga kasuwanci, neman ilimi ya kai su sassa daban-daban na duniya wanda hakan ya sa suke da al'ummomi da dama.

TRT Afrika