Daga Kevin Philips Momanyi
Shahararriyar kasuwar kayan gwanjo ta Gikomba da ke tsakiyar birnin Nairobi, tana samun hada-hadar kasuwanci a ko yaushe.
A shekarun 1960 aka kafa kasuwar, kuma ta shahara da tufafin gwanjo da ake cinikayyar su a cikinta.
A harsen Swahili – yaren da aka fi magana da shi a Gabashin Afirka, ana kiran kayan gwanjo Mitumba.
A lokacin da kuke tunkarar kasuwar, abun da ke fara yi muku maraba shi ne sautukan ‘yan kasuwa da ke kiran jama’a su zo su sayi nasu kayan, a lokacin da motocin tasi da ake kira Matatu kuma ke kai komo da fasinjoji.
Abu ne ruwan dare ka ji ‘yan kasuwar gwanjon na kiran masu sayayya da ‘Karibu' kwastoma, Mitumba kwa wingi’ wanda ke nufin ‘Barka da zuwa kwastoma, akwai kayan gwanjo da yawa a nan’.
A yaren Swahili Mitumba na nufin “Kunshin kaya” ma’ana kunshin kaya da aka daure da igiya.
Kayan da ake sayarwa a kasuwar Gikomba ba su da tsada kuma na musamman ne da ba a ko ina ake samun su ba, in ji Grace Karangu, wata da ke yawan sayen kayan. Ta bayyana kayan kasuwar da cewa suna da inganci.
Amma kuma, yadda mutum ya taya kayan ne ke sanyawa ya samu farashi mafi kyau, hakan zai sanya ka ajiye kudi sannan ka magance dabarun ‘yan kasuwar.
Ana bude kasuwar har a ranakun mako, amma ta fi samun jama’a a karshen mako inda ake samun armashi da kade-kade.
Mafi yawancin jama’ar Kenya musamman wadanda ke rayuwa a babban birnin Nairobi sun saba zuwa wannan kasuwa tun yarinta. Mutane na zuwa da iyalansu don sayen tufafi masu kyau.
“Na san wannan kasuwar tun ina karamin yaro. Shekaruna 41 yanzu. A can nake sayen duk tufafina,” in ji John Gathee, mazaunin Nairobi.
Kasuwar na jan hankalin dubban mutane – masu saye da masu sayarwa – daga Tanzania da Uganda da sauran yankunan Kenya.
Wadannan kasashe na kan gaba wajen shigar da tufafin gwanjo a Gabashin Afirka, inda Kenya ke shigar da tan 100,000 a shekara, kamar yadda gwamnati ta sanar.
Mafi yawan kayan gwanjo na Afirka na zuwa ne daga kasashen Yamma. Amma gwamnatocin Afirka na daukar matakan haramta shigar da tufafin gwanjo kasashen nasu.
Bayan tattaunawa da majalisar ministoci game da Yarjejeniyar Kasuwanci Mara Shinge a Afirka (AfCTA a Nairobi, Sakatare Janar na AfCTA, Wamkele Mene ya bayyana cewa matakin na da muhimmanci don bunkasa samar da tufafi a Afirka.
An ruwaito Mene na cewa “Matakin da majalisar ta dauka babban sako ne na cewa kasuwarmu guda daya ba za ta zama bolar tufafin da aka yi amfani da su a wajen Afirka ba.”
A wajen Joyce Ndung’u, wata ‘yar kasuwa a Gikomba, kamata ya yi a hana shiga da tufafi gwanjo nahiyar Afirka ya zama hankali mataki-mataki, saboda matakin gaggawa kan iya shafar hanyoyin samun kudaden mutane.
Ta fadawa TRT Afirka cewa “kasuwancin gwanjo ne ke rike min rayuwata. Ban san wata sana’a ba.”
Ta shawarci mahukunta da su nemo hanyoyin da suka fi dacewa don habaka masana’antun kasashensu.
Kasuwar Gikomba ba damarmakin tattalin arziki kawai take samarwa ga dubban ‘yan Gabashin Afirka ba, ta kuma zama wajen samun kudaden shiga ga gwamnatin Kenya.