Keneth Ragoji da Shirleen Wanjiru su ne suka yi nasara a gasar. Hoto/TRT Afrika

A wani daren Asabar yayin da ake sanyi a Nairobi, amma a cikin dakin taron Jami’ar Nairobi, abubuwa sun dau zafi.

An daga labule inda aka ga masu tallar kayan kawa a tsaye inda suke ta yin rawa ga wakar da ba su ji.

Sai dai karar sautin yana da karfin da zai sa jijjigar sautin ya sa su bi kidan wakar da kafafuwansu, wanda hakan yake ba su kwarin gwiwar baje kolin fasahar rawarsu.

‘Yan takara goma daga sassa daban-daban na Kenya ke gasar Sarki da Sarauniyar Kuramen Kenya ta 2023.

Wannan shi ne karo na uku na gasar al’adu da baje kolin fasaha ta kungiyar kurame ta Kenya wanda aka soma a 2018.

A daidai lokacin da suke nuna kayayyakinsu na gargajiya na Afirka, ‘yar takarar ta farko ta soma hawa kan dandamali inda take rawa kafin daga nan ta soma tafiya irin wadda ake karya kwankwaso.

Sai sauran suka biyo baya da tafiya, daya daga cikinsu na rawa a tsakiyar dandamalin da dan karamin kwando a kan kugunta.

Sai kuma wata sanye da kayayyakin gargajiya na Kalenjin regalia; wadda riga ce mai dogon hannu dauke da wuri da duwatsun ado a goshi inda ta hau kan dandamali da kwarya.

Sai ta yi kamar wasan kwaikwayo kan yadda a al’adance ake ajiye madara ta zama nono, inda ta kammala wasan nata da kurbar madarar da ke cikin kwaryar kafin ta tashi ta tafi da tafiyar karya kwankwaso.

Bebanci

Shirleen Wanjiru wadda ta kasance zakara a gasar, ma'aikaciya ce a wani wurin gyaran gashi a Kenya. Hoto/TRT Afrika

Bikin wanda aka gudanar a ranar 23 ga watan Satumba wanda ya zo daidai da Ranar Maganar Kurame ta Duniya, ya kasance biki na karshe na kuramen wanda aka shafe mako guda ana yi.

Mau’du’in wannan shekara shi ne ‘Duniya wadda kurame za su iya amfani da yaren hannu a ko ina.

A daidai lokacin da dare ya yi dare, inda masu kallo suka kagara su san wa zai samu kambun sarki da sarauniyar kurame ta bana.

Wadanda suka ci wannan gasa su ne....

Ga maza wanda ya ci wannan gasar, an kara ne tsakanin Keneth Ragoji mai shekara 29 daga yammacin kasar da kuma Collins Selian mai shekara 27 daga Gabashin kasar.

Dukansu daya, a lokacin da aka bayyana wanda ya ci gasar, Ragoji wanda a baya ya hau kan dandamalin shafe da farin alli a fuska da kirji da kafafuwa.

“Wannan ne karo na farko da nake zaune a kan wannan kujerar” kamar yadda ya nuna da yaren bebanci a lokacin da ya zauna.

Gasar ta fi zafi a tsakanin mata. Akwai takwas daga cikinsu wadanda suke son lashe gasar.

Alkalan sun amince da Shirleen Wanjiru mai shekara 24 wadda ta fashe da kuka a lokacin da ta gane cewa ita ta lashe gasar.

“Ina murna kan cewa ina da wannan kambun” kamar yadda ta bayyana da yaren bebanci. Shirleen na aiki a wani shagon gyaran gashi a wani titi da ke tsakiyar birnin Nairobi.

Shi kuma abokin nasararta Ragoji bai dade da kammala karatunsa a fannin injiniyan lantarki ba ya tuna yadda yake son tallan kawa a lokacin da yake yaro.

“Wannan mafarkina ne ya tabbata” kamar yadda ya nuna inda yake bayani kan yadda yake kallo da karanta mujallu dangane da maza masu tallan kayan kawa. Duk da haka bai taba tunanin zai taba zama kamarsu ba.

“Nakasar da nake da ita sai ta zama kamar wani abu da ke dakatar da ni amma hakan ya ba ni karfin gwiwa” kamar yadda ya kara da cewa. Wanjiru da Ragoji sun samu gurbi a bikin kurame na farko na al’ada na kasa da kasa da za a yi a birnin Dar-es-Salaam na Tanzania a watan Nuwamba.

A fadin duniya, akwai kusan mutum miliyan 430 da ke fama da nakasa inda kaso 5.5 na mutanen duniya ke da matsalar ji, kamar yadda Hukumar Lafiya ta Duniya ta tabbatar.

Samun matsalar ji za ta iya faruwa sakamakon kara mai karfi ko gado ko tsufa sakamakon ciwon kunne.

Kurmanci na kawo cikas wurin magana da mutane da kuma kawo cikas wurin ci gaban harshe ga yara. Hakan zai iya jawo wariya da kadaici da takaici.

TRT Afrika